Wata kotu a Abuja ta ce barawon tukunyar gas na girki yasha bulala

Wata kotu a Abuja ta ce barawon tukunyar gas na girki yasha bulala

- Barawon gas zai sha bulala 6

- An same shi da laifin sata da kuma an masa wa'azi ya dena sata.

An kama wani mutum mai suna Bala da laifin satar Gas na girki, amma sai yace ayi masa afuwa bazai sake ba, wai abokai na banza ne suka koya masa sata.

Wata mata mai suna Florence ce ta kai karar barawon, bayan da aka kama shi da tukunyar gas din charaf bayan ya sata, a cikin gidansu, aka kuma miqa shi ga 'yan sanda na yankin.

An tsalala masa bulalolinsa, an kuma gargade shi da kar ya sake sata, inda yayi godiya, da tuba, ya tashi ya qara gaba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel