Lauya mai tacewa ya nemi a tsige Shugaba Buhari kan wasikar da ya rubuto wa Majalisar zartarwa

Lauya mai tacewa ya nemi a tsige Shugaba Buhari kan wasikar da ya rubuto wa Majalisar zartarwa

- Ebun-Olu Adegboruwa yace furucin shugaban cewa mataimakinsa yacigaba da gudanar da lamarin kasar bayansa bazai kai mataimakin ga gaci ba

- Ayanzu haka a takaice, Najeriya babu takamaiman shugaba mai tacewa a kasa, kuma bamuda kowa a ofishin mataimakin shugaba

Wani Lauya masanin hakkin dan adam a jihar Legas, Ebun-Olu Adegboruwa, ya nema daga majalisar dattijai dasu fara tuhumar shugaba Buhari kan sakon wasikar da ya aiko wa majalisar.

A jawabinsa da NAIJ.com ta nakalto daga jihar Legas, Mr. Adegboruwa yace furucin shugaban cewa mataimakinsa yacigaba da gudanar da lamarin kasar bayansa bazai kai mataimakin ga gaci ba.

“Majibincin lamari a zahiri shine mai matsayi irin na saura, sakamakon haka mataimakin ba lallai bane ya iya tabbatarda wani ko kora wani daga aiki a sakamakon tafiyar shugaba.

“Bashida cikakken iko akan wasu ministoci, kuma bazai iya gudanar da abubuwa ba yanda ya kamata kuma baida tacewa akan shugaban ma'aikatan villa daya fitarda wasu takardu daga ofishin shugaban a Villa.

KU KARANTA: Farfesosi 3 'yan Amurka sun karbi musulunci a garin Yola

“A takaice, Najeriya babu takamaiman shugaba mai tacewa a kasa, kuma bamuda kowa a ofishin mataimakin shugaba. ofishin mai rikon kwaryar da kundin tsarin kasa ya tabbatar ya haifar da cyakuduwar makaman guri daya a sakamakon tafiyar shugaban kasar neman lafiya kasar waje.''

Shugaban ya bar kasar ne a daren Lahadi zuwa Turai kuma ya aiko da wasikarsa wa majalisar zartarwa a yau da ta kunshi bayanin wakiltar da lamarin kasa wa Osinbajo.

Zanturtukan da shugaban yayi a wasikar tasa sun zama abin tattaunawa a tsakanin yan najeriya.

Mr. Adegboruwa yace Majalisar zartarwa batada tacewa a shelantar da ccewa mataimakin shugaban kasar zai jibinci lamarin kasar ba tareda hadin guiwar majalisar majalisar dattijai ba.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel