Karya Faruk Lawan keyi akan batun kudin cin hanci na lokacin cire tallafin mai - Dan majalisa

Karya Faruk Lawan keyi akan batun kudin cin hanci na lokacin cire tallafin mai - Dan majalisa

- Batun cin hanci da rashawa na lokacin binciken cire tallafin mai ya sake tasowa

- Ana tuhumar Faruk Lawan da zuwa karbar kudin cin hanci a gidan hamshakin dan kasuwa Otedola

- An ruwaito cewa Faruk Lawan ya ce kudin suna wurin dan majalisa Adams Jagaba.

- Adams Jagaba yace karya ce kawai Honorabul din ya sheka.

- Shekaru 6 har yau babu kudin babu inda suke.

A lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ne ake tuhumar Hon. Faruk Lawan, da laifin tatsar hamshakin dan Kasuwa Otedola. Rahotanni sun ce har da video na yadda ya ringa cika aljihun sa da makudan daloli, har dubu dari shidda, $620,000. Amma kuma an nemi kudin an rasa, shekaru biyar kenan.

A baya-bayan nan, Faruku LAwan din yace ya kai ajiyar kudin ne wurin abokin zamansa na Majalisa, Adams Jagaba, inda shi kuma ya fito ya musanta, ya kuma ce hasali ma qarya ce shi Honorabul Lawal din ya shirga. Yace ba wani lokaci da Faruk Lawal yazo gidansa a talatainin dare, a watan afrilun 2012. Ya fadi hakan ne a kotu yayin da yake bada shaida.

Sarkakiyar wannan shari'a ta saka har batun ya kai haka amma an kasa gane kan batun, inda kowa ke jifan kowa da kashin kaji, su kuwa kudin sunyi batan dabo. abin kunya kuma duk da haka wadannan mutane suna da karfin fada a ji a tsakanin al'umma. ku biyo mu a shafinmu na facebook da twitter don karin bayani.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare
NAIJ.com
Mailfire view pixel