Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

- Babbar kotun tarayya ta yanke ma Bala Muhammed hukuncin zaman gidan yarin Kuje

- Kotun ta daure Bala Muhammed ne sakamakon zargin badakalar miliyan 500 da EFCC keyi masa

A ranar larabar nan 10 ga watan Mayu ne wata babbar kotu dake zamanta a babban birnin tarayya ta umarci a daure mata tsohon ministan babban birnin tarayya Bala Mohammed a gidan yarin Kuje, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Umarnin kotun ya biyo bayan shigar da karar tsohon ministan da hukumar yaki da cin hanci da almundahana, EFCC tayi ne gaban kotun kan tuhumarsa da take yi da karkatar da kudaden al’umma tare da cin amanar kasa.

KU KARANTA: Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

EFCC ta gurfanar da Bala Muhammed ne kan badakalar amsan cin hanci na naira miliyan 500 yayin dayake rike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja.

Kotu ta umarci a ɗaure mata tsohon minista Bala Muhammed a gidan yari

Tsohon minista Bala Muhammed

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito EFCC na tuhumarsa kan rashin bayyana kadarorin da suke karkashin mallakinsa, sai dai Bala Muhammed ya musanta zarge zargen da EFCC ke yi masa.

Bayan sauraron bangaren lauyoyin EFCC dana tsohon ministan, sai alkali mai shari’a Abubakar Talba ya dage sauraron karar zuwa 12 ga watan Mayu don yanke hukunci kan bukatar bada beli da Bala Muhammed yayi.

Amma kafin zuwan ranar cigaba da sauraren karar, mai shari’a Talba ya umarci da a daure masa tsohon minista Bala Muhammed a gidan mari dake Kuje, a babban birnin tarayya Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shari'ar EFCC da Andrew Yakubu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel