Anyi aringizon kasafin kuɗin bana da naira miliyan dubu 149 a majalisa

Anyi aringizon kasafin kuɗin bana da naira miliyan dubu 149 a majalisa

- Majalisar dokokin Najeriya ta karbi kasafin kudin bana daga kwamitocin ta

- Sai dai majalisar tayi canje canje da sauye sauye a kasafin kudin na bana

Majalisun dokokin kasar nan sun yi wasu canje canje a cikin kasafin kudin shekarar 2017 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika musu a watan Disambar bara.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje ya bayyana cewar kwamitinsa ta kammala ayyukan da aka daura mata.

KU KARANTA: Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

Sai dai jimillan kasafin kudin ya haura zuwa naira triliyan 7, 441, 175, 486, 758, kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai Mustapha Madawaki yace majalisar ta yi canza kudaden da aka kayyade ma manyan ayyuka daga naira triliyan 2.24 zuwa naira triliyan 2.17.

Anyi aringizon kasafin kuɗin bana da naira miliyan dubu 149 a majalisa

Lokacin da Buhari ya mika kasafin kuɗin bana ga majalisa

Sa’annan sun kara kudaden hidimar yau da kullum daga naira triliyan 2.98 zuwa naira triliyan 2.99, tare da kara kudaden da aka ware ma bangaren aika kudade daga naira biliyan 419 zuwa Naira 434, 412, 950, 249.

Bugu da kari NAIJ.com ta ruwaito majalisar ta yi kari akan kudaden biyan bashi daga naira triliyan 1.66 kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata zuwa naira triliyan 1.84.

Yayi dayake yi ma yan jaridu karin bayani, mai magana da yawun majalisar dattawa, Sanata Sabi Abdullahi yace zasu tabbatar da kasafin kudin bana tare da dukkanin cikakkun bayanan sa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai majalisun dokoki nada amfani kuwa, kalla?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel