Toh fa: Kotu ta hana Andrew Yakubu miliyoyin dalolinsa

Toh fa: Kotu ta hana Andrew Yakubu miliyoyin dalolinsa

- Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon manajan kamfanin NNPC inda ya nema a mayar masa da miliyoyinsa da ke hannun hukumar EFCC

- Yakubu ya nemi a watsar da umarnin da kotun ta bai wa hukumar EFCC ta'annati cewa ta damkawa gwamnatin tarayya kudin

- Mai shari'a ta ce a shari'ance dokar kasa ta bai wa EFCC damar neman umarnin a mika kudin ga gwamnati.

Wata babbar kotu a Kano ta ki amincewa da bukatar da tsohon manajan kamfanin mai na Najeriya NNPC, Andrew Yakubu ya shigar, inda ya nemi da a watsar da umarnin da kotun ta bai wa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati cewa ta damkawa gwamnatin tarayya kudin.

A watan Fabrairu ne kotu ta bai wa hukumar EFCC damar mallakawa gwamnati sama da dala miliyan 9.8 da aka samu daga gidan Mista Yakubu a Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Dala tayi kundumbala a kasuwar canji

Mai shari'a Zainab Abubakar ce ta yanke hukunci kan bukatar wadda lauyan Mista Yakubu ya shigar, inda ta ce kotu tana da hurumin sauraron karar ba kamar yadda lauyan ya nuna cewa hakan ba daidai ba ne.

Toh fa: Kotu ta hana Andrew Yakubu miliyoyin dalolinsa

A lokacin da hukumar EFCC ke fitar da miliyoyin daloli a gidan Andrew Yakubu

NAIJ.com ta ruwaito cewa mai shari'ar ta kuma ce bukatar Mista Yakubu da ke neman a yi watsi da shari'ar ba ta da wata madogara a shari'ance, kuma dokar kasa ta bai wa EFCC damar neman umarnin a mika kudin ga gwamnati.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel