Malaman makaranta sun fara yajin aikin sakamakon rashin albashin wata 9 a Bayelsa

Malaman makaranta sun fara yajin aikin sakamakon rashin albashin wata 9 a Bayelsa

- Malamai a jihar Bayelsa sun shiga yajin aikin da babu ranar dawowa matukar ba'a biya su hakkokinsu ba

- An shawarci malaman da su yi azumin kwanaki bakwai domin samun nasara

Malaman makaratun firamari a jihar Bayelsa sun fara yajin aikin sai baba-ta-ji don nuna bacin ransu da rashin samun albashin watanni 9, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Malaman sun shiga yajin ne a ranar Litinin 8 ga watan Mayu, bayan sun yi watsi da tayin da gwamnatin jihar ta musu na biyansu albashin wata daya daga cikin watannin taran, inji rahoton Kamfanin dillancin labaru, NAN.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

Kungiyar malamai reshen jihar Bayelsa ya bayyana goyon bayanta ga yajin aikin malaman, cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata ta bakin shugabanta Kalama Toinpre, wanda yace ya zama dole malaman su dauki wannan mataki don neman hakkinsu.

Malaman makaranta sun fara yajin aikin sakamakon rashin albashin wata 9 a Bayelsa

Kungiyar malamai

Shugaban kungiyar ya umarci malaman dasu yi zamansu a gida har sai gwamnati ta biya su albashin akalla watanni uku kafin su fara wani tattaunawa da gwamnatin. Sa’annan shugaban ya bukaci hukumar ilimi ta bai daya, SUBEB na jihar Bayelsa data aiwatar da tsarin karin girma da aka yi ma malaman jihar.

Majiyar NAIJ.com tace bugu da kari, shugaban ya shawarci malaman dasu fara azumin kwanaki 7 don samun sa’a akan matsalar, inda ya gargadi gwamnatin jihar cewar idan bayan sati biyu gwmanati bata yi wani hubbasa ba, makarantun sakandari ma zasu shiga yajin aikin don mara ma abokan aikinsu baya.

Sai dai a wani labarin, kwamishinan kananan hukumomin jihar ya sanar da biyan albashin watan Afrilu, don haka ya shawarci malaman da su janye yajin aikin da suka fara, amma malaman sun yi watsi da umarnin nasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga sabon sana'a fa a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel