Hukuncin shekaru 2 ga gwamna da ya musanta ayar Qur'ani

Hukuncin shekaru 2 ga gwamna da ya musanta ayar Qur'ani

- Kasar Indonisiya tafi kowa yawan Musulmi a duniya, tana da yaruka akalla 15, tana da dokokin haramta yin sabo, kuma ta haramta akidar mulhidanci wato atheism, tun a 1969

- Gwaman ya rasa sake samun goyon bayan jama'a a takara ta gwamnan jihar Jakarta, babban birnin kasar, bayan da ya yi sabo a lokacin yakin neman zabe, wanda ya jawo ayoyin da masu adawa da shi ke amfani da su, don muzanta shi, a matsayinshi na kirista

- An yanke masa hukunci zaman kurkuku na shekaru 2

A can kasar Indonesiya, wani Gwamna ya harzuka jama'a inda har suka fito tituna suna zanga-zanga domin a bi musu hakkinsu, na batanci da suke zargin Gwamnansu Kirista yayi a lokacin neman sake zarcewa a karo na biyu.

Ya sami damar zama gwamnan babban birnin kasar ta Indonesiya, duk da cewa dan asalin qabilar mutan sin ne, kuma kirista ne, a yayin da kusan kashi 90 bisa dari na jama'ar kasar duk musulmi ne.

Gwamna Ahok, ya fadi zaben tazarce, ya kuma sami hukuncin dauri na shekaru biyu a gidan kurkuku, saboda sabo da suka ce yayi, a lokacin da yake inkari akan wasu ayoyi da 'yan dayar jam'iyyar adawar suka yi amfani dasu, domin muzanta shi, a matsayinsa na wanda ba musulmi ba.

Ya dai karyata ayar ta kur'ani, inda yace ayar bata yi masa adalci ba, kuma bai kamata su 'yan adawa suyi amfani da ita ba, a lokacin yakin neman zabe. Amma shaihunnan malaman babban birnin, sun kira gangami, domin a nuna rashin amincewa da zantukan nasa masu cike da batanci da ko in kula da jama'ar da suka zabe shi a matsayin gwamnansu a shekakar 2014.

A karshe dai, alkali ya rage hukuncin da akai masa, daga zaman kurkuku na shekaru biyu, zuwa shekara daya a daurin talala, wanda a gida zaiyi, na jeka-gyara halinka. hakan zai fara ne in ya kammala mulkinsa na Gwamna a kasar ta Indonesiya ta nahiyar Asiya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel