Shugabancin Ali Sheriff na PDP daga Allah ne - Wani jigon jam'iyyar

Shugabancin Ali Sheriff na PDP daga Allah ne - Wani jigon jam'iyyar

- An sami rabbabuwar kawuna a Jam'iyyar PDP tun bayan shan kaye da suka yi a zabukan 2015

- Bangarorin suna da shugabanni wadanda basa ga-maciji-da-juna

- Ana dab ta fara shirye-shiryen fara zabukan cikin gida a jam'iyyu, domin tunkarar zabuka na 2019

Wani jigo a jam'iyyar PDP, yace shugabanci na jam'iyyar, bangaren tsohon Gwamna Ali Modu Sheriff, zabi ne daga Allah, don haka kowanne dan adawa da mulkin ya hakura ya bar tantama da ja. Bernard Mikko, wanda yake bin shugabancin Ali Modu Sheriff, yace Allah ne ya turo Ali Sheriff din domin ya tsarkake halin tsageranci da rashin da'a a cikin jam'iyyar.

Ya kara da cewa, duk abubuwan da shi Ali Sheriff din yake yi, yana yi ne domin kawo sabon tsari, da kuma dawowa da jam'iyyar tagomashinta, a lokutan zabuka da zasu zo nan gaba.

Ya sake kuma caccakar jam'iyya mai mulki a matsayin wadda bata iya mulki ba, wadda yace su zasu ga bayanta a zabuka masu zuwa.

Shugabancin Ali Sheriff na PDP daga Allah ne - Wani jigon jam'iyyar

Ali Modu Sheriff na PDP

Shi dai wannan jigo, yace babu jam'iyyar da ta kai jam'iyyar tasu ta PDP iya yaki da cin hanci da rashawa. Ya bada misalai na cewa, mulkin su na PDP ne ya kawo ICPC da EFCC, wanda kuma a watannin mulkinsu na farko, bayan zabukan 1999, suka sauke kakakin majalisa, dalilin shara ta da yayi game da yawan karatun da yayi.

Ya kuma buga misalai na yadda suke ta sauke shuwagabannin Majalisar dattijai, domin zargin cin hanci. Sai ya rufe da cewa, shirme ne a zaci, cewa in sun dawo mulki, baza su iya yaqi da cin hanci da sata a matakin gwamnatin tarayya ba.

A kwanakin nan dai, da yawan zargi da kame na kudade da ake yi na sata, mafi yawan wadanda ake zargin, sun fito ne daga jam'iyyar PDP wadda ta bar mulki a 2015.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel