Masu matsalar makanta 321 ne suka yi rajistar jarrabawar share fagen shiga Jami'a.

Masu matsalar makanta 321 ne suka yi rajistar jarrabawar share fagen shiga Jami'a.

- Masu matsalar ido suna fuskantar matasoli a harkar karatu a kasar nan

- Anyi kira ga jami'o'in kasar nan da su kula da nakasassu dake neman ilmi a makarantunsu

- An sami karuwar nakasassun dake shiga fagen harkar rajistar jarrabawar JAMB, ta share fagen shiga Jami'a

Dalibai masu niyyar shiga karatun kwasa-kwasai a jami'a a Najeriya sun yi rajistar jarrabawar JAMB, wadda da ita ne ake samun admishin na shiga karatu, an kuma sami karin yawan masu rajistar a bana, inda aka fayyace cewa daga cikinsu, an sami karin yawan nakasassu, masu matsalar ido, da zasu zauna zana jarrabawar ta computer.

A bana dai an sami mutum 321 da zasu yi jarrabawar masu matsalar idanu, wanda ya dara na bara da ke a 260. Dalibai miliyan daya da rabi ne dai suka yi rajistar ta jaraabawar. Shugaban jarrabawar, ya ce a wannan karon zasu yi iya kokarinsu na rage korafe-korafe da ake samu a baya, zasu hada su masu nakasar, a wuri daya, ko Legas ko Abuja, domin su yi jarrabawar da sabbin kwamfutoci da aka shirya musamman domin hakan.

Shugaban yace zasu yi musu gwaje gwaje da tsari kafin su yi jarrabawar, domin tantance su, sa'annan ya yi kira ga jami'o'i da su bada tasu gudummawar wajen karbar wadannan dalibai, da sama musu muhallin karatu da ya dace. Za'a yi jarrabawar ne a 13 ga watan mayu na banan nan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel