Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

- Daruruwan jama'a ne ke mutuwa a tekun Libya akan hanyar tsallakawa nahiyar Turai

- Kasar Italiya na kokarin ganin ta ceto da dama daga cikin wadanda suka nutse a tekun

Sama da bakin-haure 200 ake fargabar mutuwarsu a tekun Bahar-rum sakamakon nutsewar jirgin da ke dauke da su a kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai, inji rahoton rediyan Faransa.

Wasu mutane da aka ceto sun shaida wa hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya cewa, daruruwa sun fada ruwa a lokacin da kananan jiragen roba da ke dauke da su suka fara sacewa.

KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

Majiyar NAIJ.com ta bayyana ko a ranar Asabar da ta gabata, an ceto gawarwaki uku daga cikin mutane 60 da suka nutse a tekun kuma jirgin ya bar gabar tekun Libya dauke da mutane 120.

Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

Kifawar jirgin ruwa dauke da jama'a

A wani labarin kuma, hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kimanin bakin haure146 sun bace bayan kwale-kwalensu ya kife da su a tekun Mediterranean jim kadan da barin Libya.

Wani dan asalin kasar Gambia da aka ceto daga hatsarin ya ce, akwai kananan yara da mata masu juna biyu da ke cikin kwale-kwalen.

Ana fargaban mutuwar bakin-haure yan Afirka mata, kananan yara da jarirai a tekun Libya

Jirgi cike da jama'a a tekun Libya

Mutumin ya ce, Fasinjojin sun hada da ‘yan Najeriya da Mali da Gambia. Hukumomi sun bayyana, akalla ‘yan gudun hijira 590 ne suka rasa rayukansu ko kuma suka bace a gabar tekun Libya a cikin wannan shekarar.

A nata bangaren, kasar Italiya tace, tayi wa ‘yan gudun hijira dubu 23 rajista a cikin wannan shekarar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ba maraya sai rago, kalli sana'ar da wata mata keyi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel