Da dumi-dumi: Yan fashi sun farwa matafiya a babbar hanyar Abuja-Keffi

Da dumi-dumi: Yan fashi sun farwa matafiya a babbar hanyar Abuja-Keffi

- Yawan yan fashin zasu kai goma, a yayin da biyar daga cikinsu sun fito ne daga jeji dauke da muggan makaman da suka kunshi bindigogi da adduna

- Fashin ya auku ne kimanin karfe goman safiyar yau a kusa da wani kauye da ake kira Barde

Wasu yan fashi da makami da ake zargin makiwata shanu ne daga fulani sun farwa matafiya a yau laraba a hanyar Abuja-Keffi,sun tafi da kayaryakin kwace da suka kunshi wayoyin salula da kudadefashin ya auku ne kimanin karfe goman safiyar yau a kusa da wani kauye da ake kira Barde, bayan an wuce Gidan Waya a dazata kai Jihar Kaduna kusa da Jos babban birnin jihar filato.

Yawan yan fashin zasu kai goma, a yayin da biyar daga cikinsu sun fito ne daga jeji dauke da muggan makaman da suka kunshi bindigogi da adduna suka tsayarda motoci tareda umartar fasinjoji da su rusuna su kwanta a kasa.

wakilan mu makusanta gurinda abin ya faru sun nakaltowa NAIJ.com cewa sunga mata yan kasuwa a firgice yayinda barayin kemusu barazan da bindigogi.

KU KARANTA: Manyan dalilan da suka suka sanya Boko Haram sako 'yan matan Chibok

Fashin ya auku ne tsakanin matsayoyin yansanda biyu dake kan babban hanyar.

Barayin sun tattara nasu ya nasu sun shige jeji bayan mintina talatin da cin nasara a aika-aikan da suka yi lokacin da suka Hango tahowar sojoji tafe.

wasu daga wadanda abin ya cika dasu sun bada jawabin cewa barayin fulanawa ne a sakamakon yaren da akaji suke yi yayin fashin.

Wata daga matan da ke kasuwanci wa maigidanta a rahoton NAIJ.com ta barke da hawaye bayan rasa makudan kudi da tayi sakamakon aika-aikan da ya auku. Ta nemi wakilan yada labarai dasu ceceta gun kai bayanin abinda ya auku wa maigidan nata don samun kubuta daga fushinta.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel