Wani uba ya rataye 'yarsa mai shekaru 8 domin ta yaga masa takardar sakin aure

Wani uba ya rataye 'yarsa mai shekaru 8 domin ta yaga masa takardar sakin aure

Wani magidanci ya yi kokarin hallaka yarsa mai shekara 8 kacal da haihuwa domin ta kekketa takardar da yake kokarin rubutawa ta sakin matarsa inda yarinyar ta mutsistsike takardar tare da fasa masa kwalbar barasa.

Mahaifin ya sauke haushinsa kan yarinyar inda ya daure ta tamau da igiya tare da zare mata wando ya rataye ta a saman silin dakinsa tana lilo, sannan kuma ya dauki hoton bidiyon yarinyar ya tura wa mahaifiyarsa ta kalla.

Wani uba ya rataye 'yarsa mai shekaru 8 domin ta yaga masa takardar sakin aure

Wani uba ya rataye 'yarsa mai shekaru 8 domin ta yaga masa takardar sakin aure

NAIJ.com ta samu labarin cewa kallon bidiyon yarinyar ke da wuya, uwar ta sanar da Yan sanda inda suka garzayo a guje gidan mutumin suka ceci yarinyar.

Wani Dagaci garin Guangzhou dake a lardin Sichuan kasar China ya ce lallai har in an gama yi wa mutumin gwajegwajen kwakwalwa, har aka tabbatar lafiyarsa garau, to lallai zai dandani hushin hukuma.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel