Aikin gidauniyar tallafawa jihohin Arewa maso gabas

Aikin gidauniyar tallafawa jihohin Arewa maso gabas

- Gidauniyar tallafawa jihohin arewa maso gabas da adin gwiwar gwamnatin jihar Adamawa sun yi alkawarin sake gina wasu asibitoci a jihar

- Babban daraktan gidauniyar ya ce an zabi asibitocin ne saboda gudunmawar da suka bayar wajen jinyar wadanda suka jikkata a hare-haren ta’addancin Boko Haram

- Kungiyar ta ce ta tallafawa dalibai 12,000 da kayayyakin da suka bukata don karatu a yankin Mubi da Hong

Gidauniyar tallafawa jihohin arewa maso gabas da gwamnatin jihar Adamawa, sun saka hanu kan yarjejeniyar aiki kafada da kafada ta naira miliyan 40 don sake gina asibitocin Michika da Mubi.

Da yake mikawa gwamnan jihar Adamawa sanata Muhammad Umaru Jibirilla, takardar kudin a ofishinsa, babban daraktan gidauniyar wadda Janar T. Y Danjuma ke shugabanta, Farfesa Sunday Ochoche, ya ce an zabi asibitocin biyu ne bayan la'akari da gudunmawar da suka bayar wajen jinyar wadanda suka jikkata a hare-haren da Boko Haram suka rika kaiwa mazauna yankin.

Baya ga gyaran asibitocin, akwai manyan ayyukan da gidauniyar za ta aiwatar da suka hada da sake gina sakatariyar ta karamar hukumar Michika da kuma gina makarantu bakwai a kananan hukumomin Mubi da Hong. Farfesa Ochoche, ya ce bayan gidauniyar ta tallafawa dalibai 12,000 da kayayyakin da suka bukata don karatu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Farfesa Sunday Ochoche ya ce akwai matakai da sharudan da gidauniyar ta shimfida na aiwatar da ayyukan ta da kudin da take baiwa jihohi gudumawa don gudun Kada su karkatar su ta wata hanya.

Gwamnan jihar Adamawa sanata Muhammadu Umaru Jibrilla, ya ce za a dauki lokacin mai tsawo ana gyara, saboda barnar da yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka aikata, don haka jiharsa ke ci gaba da neman Karin tallafi na samar da muhimman kayan rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

A kananan hukumomin Gombi da Maiha, gidauniyar ta zabi marayu 1,000 wadanda ta dankawa wasu iyaye amanar kulawa da rayuwa da ilimantar da su ta hanyar baiwa kowanne iyali tallafin naira 14,000 kowace wata.

Daya daga cikin iyayen Mallam Abba Mohammed, a karamar hukumar Maiha ya ce wannan tallafin zai taimaka wajen renan shugabanni na gari daga cikin marayun nan gaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali bidiyon wasu yara da suka tsira daga hannun 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel