Dalibai 1, 736, 571 ne sukayi rijistan JAMB a shekaran nan – Shugaban JAMB

Dalibai 1, 736, 571 ne sukayi rijistan JAMB a shekaran nan – Shugaban JAMB

Hukumar gudanar da zaben shiga jami’a wato Joint Admission and Matriculation Board (JAMB) ta bayyana cewa jimillan dalibai 1, 736, 571 (Miliyan 1 da dubu dari bakwai da talatin da shida, da dari biyar da saba’in da daya.

Shugaban hukumar JAMB, Is-haq Oloyede, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Bwai, inda yake bayanin shirye-shiryen jarabawan wannan shekara.

Mr. Oloyede, wanda yayi wannan bayani filla-filla akan wadanda sukayi rijista yace wannan lamba ya nuna banbancin da shekarun baya.

Dalibai 1, 736, 571 ne sukayi rijistan JAMB a shekaran nan – Shugaban JAMB

Dalibai 1, 736, 571 ne sukayi rijistan JAMB a shekaran nan – Shugaban JAMB

A jarabawan bara, dalibai 1, 272, 284 ne suka zauna jarabawan.”

“Lamban wadanda zasu rubuta ya karu da 464, 287 idan aka hada da na shekaran da ya gabata 1, 272, 284,”.

Yace jihar Imo ce mafi yawa masu yawan dalibai 101, 868; sai jihar Osun 88, 655; Oyo 87, 811 da Ogun 81, 349.

KU KARANTA: Manufofin Buhari da Amurka daya ne

Sauran sune Delta – 81, 108, Anambra – 77, 253, Kaduna – 72, 104, Kano – 70, 276, Kogi – 70, 150 da Benue – 68, 916.

Yace jimillan dalibai maras gani 321 ne kuma an shirya musu sosai kan yadda zasu rubuta jarabawansu.

Yace a wannan shekaran, za’a fadada wuraren rubuta jarabawan zuwa 624 sabanin 524 na shekaran da ya gabata.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel