Zaben Osun: Ban dauki kowa a matsayin magaji na ba – Gwamna Rauf Aregbesola

Zaben Osun: Ban dauki kowa a matsayin magaji na ba – Gwamna Rauf Aregbesola

- Gaba da zaben gwamnan jihar Osun na shekara 2018, Gwamna Rauf Aregbesola ya ce, har yanzu ba bai dauke kowa a matsayin magajin shi ba.

- Gwamnan yayi wannan bayanin ne a wani shiri tattaunawa da ake kira da su: ‘Ogbeni Till Daybreak’ wato ‘Ogbeni Zuwa Safiya’ a ranar Asabar a Osogbo.

NAIJ.com ta samu Aregbesola, ya ce ba gaskiya bane cewa zaban wanda zai gaje shi a zaben shekara 2018 na janyo wa jam’iyyar na su na APC barazana a jihar.

“Babu wani bangare na jam’iyyar na mu da ke fuskantar barazana game da wanda zai gaje ne a karshen mulki na.

“Kan mu na hade har yanzu, sannan kuma muna aiki sosai wajen ganin jam’iyyar ta cigaba.” a cewar shi.

Gwamnan, duk da haka, ya bayyana cewa babu jam’iyyar adawa a jihar iya tsayayya APC a shekara ta 2018 zaben gwamna.

“Idan har jam’iyyar adawar ta jahar na fuskantar matsaloli tare da rashin tsari, ina za mu ji tsoron zaben 2018? Gwamnan ya yi tambaya.

Zaben Osun: Ban dauki kowa a matsayin magaji na ba – Gwamna Rauf Aregbesola

Zaben Osun: Ban dauki kowa a matsayin magaji na ba – Gwamna Rauf Aregbesola

KU KARANTA: Kasar Amurka ta bayyana goyon bayan ta ga Buhari

Ya kuma yi bayani game da jita-jitar da ke cewa gwamnan na shirin fitowa takaran a zaben sanatoci a matsayin sanata wanda zai wakilci mazaban Legas ta yamma a shekara 2019. Aregbesola ya ce bai da wannan ra’ayin tukuna.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar, Mr Gboyega Famodun, wanda ya ba gwamna damar yin bayani game da zaben gwamnan 2018, inda ya kara bayyana cewa, jam’iyyar ba ta zaba wanda zai fito dan takaran gwamna ba har yanzu.

“Babu wani takamamen da takara gwamnan daga jam’iyyar a yanzu dai da na sani” inji gwamnan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel