Daya daga yan Matan Chibok da taki dawowa ; Cikin farinci nake tareda Mijina a inda nake

Daya daga yan Matan Chibok da taki dawowa ; Cikin farinci nake tareda Mijina a inda nake

- Mai magana da yawun shugaba, Garba Shehu yace masu jihadin sun yarda da bada yan matan 83 a karon farko daga yan matan da aka kame a kauyen Chibok, toh amma daya daga cikinsu ta ja kujerar naki gun nuna ita bazata biyo yan'uwan nata gida

- Elizabeth Pearson, wata kwararriyar mai bincike akan yan Boko Haram ta fadi cewa yar budurwar Chibok da ta ki dawowa daga hannun yan Boko Haram din na nuna bata cikin wulakanci da fuskantar tsangwama ne daga garesu

Yaya daga yan matan makarantun 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar 2014 ta ki kasancewa tared yan'uwanta a yayin fansosu a sakamakon aure da ke tsakaninta da daya daga yan ta'adda. bayanin ya nuna tsasirantuwar barbarar tunani da mutanen sukayi musu.

Kungiyar ta Boko Haram suna amfani da kame mutane ne a matsayin makamin yakar gwamnati don tabbatar da daularsu dasuke kokarin yi tun shekaru takwas baya 2009, wanda yayi sanadin rasa rayuka 20,000 Najeriya kadai.birsunonin nasu yan mata buduri ne sukafi yawa,sannan matasa,mata.

Mai magana da yawun shugaba, Garba Shehu yace masu jihadin sun yarda da bada yan matan 83 a karon farko daga yan matan da aka kame a kauyen Chibok, toh amma daya daga cikinsu ta ja kujerar naki gun nuna ita bazata biyo yan'uwan nata gida baya ba sakamakon dadin zama da takeji da mijinta daga yan ta'addan.

An sako Ashirin da daya daga yan matan a watan Oktoba shekarar da ta wuce; an samu uku da suka kwato kansu daga tsaron boko haram din. tattaunawa na gudanuwa akan sauran yan matan 113 da suka rage.

KU KARANTA: Rikici: Yadda IPOB, MASSOB na shirin yin bikin rana Biyafara da zai dauki mako daya 1

Daga jawaban tsararrun yan matan da aka fanso na nuna cewa suna fuskantar abubuwa dayawa na kece iyaka da rashin mutunci kamar fyade, tsangwama, bautarwa, bugu da sauransu.

Elizabeth Pearson,wata kwararriyar mai bincike akan yan'Boko haram ta fadi cewa yar budurwar chibok da ta ki dawowa daga hannun yan boko haram din na nuna bata cikin wulakanci da fuskantar tsangwama ne daga garesu, daga abinda muka sani sauran na cikin akasin hakan.Ba kowacca alaka ce take mummunar alaka ba tsakanin yan boko haram din da yan matan, don wasu daga cikinsu na da kyautatawa.

An fitarda jerin sunayen yaran a ranar Lahadi tareda daukar hotunansu don hadashi da na asali don fayyacewa da tantancewa a chibok. baya hakan ne yanuwansu da sauran jama'a suka tayasu murna da farinciki a yayinda tantancewar ta tabbata sune.

Kungiyar kare haqqib bil'adama ta tukhumi gwamnati da shiga haqqin yan matan ta hanyar lissafo sunayensu da hotunansu bayan sakosu, ta hanyar nuna cewa hana na iya kara haifar da damuwa ko jin kunya a garesu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel