Tashin farko: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

Tashin farko: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

– Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya sauya lokacin taron Majalisa

– Farfesa Yemi Osinbajo ya maida lokacin baya

– Dama can Osinbajo ke jan taron lokacin Shugaba Buhari bai da lafiya

A kowace Laraba ake yin taron Majalisar zartarwa watau FEC a fadar shugaban kasa.

An dauki kusan wata guda Shugaba Buhari bai iya halartar taron ba.

Yanzu haka Shugaban kasa na rikon-kwarya ya canza lokacin taron.

Tashin farko: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

Osinbajo zai rike Kasar bayan tafiyar Buhari

Yanzu haka NAIJ.com na da labarin cewa ana can ana taron Majalisar zartarwa watau FEC inda Osinbajo ke jan ragama. Wannan ne dai karo na farko da shugaban kasar na rikon kwarya ya gana da Minstocin kasar.

KU KARANTA: Abubuwan da Osinbajo ya fara yi da hawan sa mulki

Tashin farko: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

Osinbajo da wasu Ministoci a wani taro

An saba yin taron ne karfe 11:00 na safe sai dai shi Farfesa Osinbajo yayi baya da lokacin zuwa 10:00 na safen. An dai yi makonni Osinbajo ne ke jagorantar taron saboda rashin lafiya shugaba Buhari wanda yanzu ya bar kasar domin ya ga Likita.

Kuna da labari cewa wasu Sanatoci da manyan kasar na kokarin amfani da damar rashin lafiyar Muhammadu Buhari su sauke sa daga kujerar shugaban kasar sai dai har yanzu ba mu tabbatar da gaskiyar maganar ba.

Tashin farko: Osinbajo ya dauki matakin farko bayan tafiyar Buhari

Ministoci a wani taro kafin tafiyar Buhari

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Lai Mohammed ya ba Najeriya kunya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel