Manyan dalilan da suka suka sanya Boko Haram sako 'yan matan Chibok

Manyan dalilan da suka suka sanya Boko Haram sako 'yan matan Chibok

- An bayyana dalilan da suka sanya kungiyar Boko Haram sako yan matan Chibok

- Gwamna Kashim Shettima ya bayyana mutuncin shugaba Buhari a matsayin daya daga cikin dalilin sako yan matan Chibok

Wata majiya da ke kusa da mayakan Boko Haram ta bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta yi musayar ‘yan matan Chibok 82 da wasu kwamandojin kungiyar guda uku, inji rahoton gidan jaridar AFP.

Wannan na zuwa ne bayan ma su shiga tsakani, sun shafe akalla makwanni shida suna jagorantar yarjejeniyar musayar tsakanin bangarorin biyu kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa

Rahotanni sun bayyana, murkushe Boko Haram da kuma tsagewar kungiyar gida biyu gami da rashin lafiyar shugaban Najeriya Muhd Buhari sun taimaka wajen sakin ‘yan matan na Chibok 82 da suka shafe fiye da shakaru uku a hannun mayakan Boko Haram.

AFP ta rawaito majiyoyin na cewa, Abubakar Shekau ya rasa kwamandojinsa da dama a wani farmaki da aka kai wa gungunsu a ranar 28 ga watan Afrilu a kauyen Balla, abin da ya sa ya bukaci maye gurabensu da wasu mayakan.

Manyan dalilan da suka suka sanya Boko Haram sako 'yan matan Chibok

Yan matan Chibok

Majiyoyin tsaro sun ce, an mika ‘yan matan ne ga wasu jami’an kungiyar bada agaji ta Red Cross a wani daji da ke kusa da garin Banki, a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Majiyoyin sun kara da cewa, an yi ta samun kwan –gaba kwan-baya tsakanin gwamnatin Najeriya da Boko Haram kafin a cimma yarjejeniyar musayar yan matan da mayakan Boko Haram dake hannun gwamnati.

Manyan dalilan da suka suka sanya Boko Haram sako 'yan matan Chibok

Kashim Shettima

A wani hannun kuma, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewar mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a idon duniya ne yayi dalilin sako yan matan na Chibok, inda yace da ba don mutuncin Buhari ba, da kasashen waje da suka shiga tsakani basu sa baki ba.

Shettima yace “Mutuncin Buhari ne ya sa kasashen Turai da Amurka ke tallafa ma Najeriya a yaki da Boko Haram, sa’annan dole ne a jinjin ma sojoji da yan sa kai dake yaki da Boko Haram, suma sun bada gudunmuwa wajen yarjejeniyar.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mawuaycin halin da iyayen yan matan Chibok suke ciki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel