Najeriya muhimmiyar abokiyar alakan kasar Amurka ce – Jakadan Amurka

Najeriya muhimmiyar abokiyar alakan kasar Amurka ce – Jakadan Amurka

Mataimakin diraktan ofishin jakadar kasar Amurka akan harkokin Afrika ta yamma, Mr Nathan Holt, yayi bayani cewa Najeriya bazata gushe babban abokiyar alakar kasar Amurka ba.

Holt,wanda yayi wannan bayani a birnin Washington D.C. ta wata hira yace Najeriya na da muhimmiyar amfani da nahiyar Afirka.

Yace: “Lallai fa Najeriya muhimminyar abokiyar alakar Amurka ce saboda itaca kasa a nahiyar Afrika mafi yawan jama’a, kuma dubi ga kudin man fetur, itace mafi girman tattalin arziki ko na biyu a nahiyar."

Najeriya muhimmiyar abokiyar alakan kasar Amurka ce – Jakadan Amurka

Najeriya muhimmiyar abokiyar alakan kasar Amurka ce – Jakadan Amurka

“Da yawan jama’a na 182 million, ana sa ran Najeriya zata kara yawa zuwa 400million a shekaru masu zuwa."

“Najeriya na da tasiri sosai kamar yadda kuka sani, ba a tattalin arziki kadai ba, har a kafin soja.”

“Kuma zan kara da cewa tanada halayen demokradiyya na yancin yan jarida da kuma addini, wanda ya taimaka wajen karfinta da hakuri,”

KU KARANTA: Yadda Aku ya hada rigima tsakanin mata da miji

Game da cewarsa, alakar Najeriya da Amurka ya wuce alaka kawai, ya zama kawance.

“Najeriya wuri ne mai muhimmanci garemu kuma mun san tana fuskantan kalubale da yawa.

“Mun san cewa ba abu bane mai sauki wajen dakile wadannan kalubale."

“Nasarar Najeriya ba ta Najeriya kadai ce ba, amma ta makwabtanta da kuma duniya ga baki daya. Abun farin cikin shine mun zagaya kasashe da dama amma bamu samu masu munafa irin tamu kamar Najeriya ba.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel