Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

- Sarkin Kano Muhamamdu Sunusi ya tausaya ma wani mara lafiya dake fama da ciwon koda

- Sarkin ya biya naira miliyan shidda da ake nema don yi ma mara lafiyar aiki

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya dauki nauyin mahaddacin alkur'anin nan, Na’if Isma’il da aka ce zai a yi wa dashen koda, kamar yadda Sa’adatu Baba Ahmed ta bayyana.

A kwanakin baya ne aka fara neman taimako don tallafa ma wani mahaddacin Qur’ani da kudi don ayi masa dashen koda.

KU KARANTA: Yadda Aku ya fallasa mua’malar Magidanci da ýar-aiki ga Uwargida

Ganin haka ya sanya mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II yanke shawarar zuwa duba mara lafiyar da kansa, inda yayi alkawarin zai biya masa naira miliyan 6 da asibitin Aminu Kano suka bukata “Domin ba zamu bar mahaddacin alkur'ani a cikin halin ko in kula ba.” Kamar yadda Sarkin ya fada.

Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

Sarki Muhammadu Sunusi tare da mara lafiyan

A safiyar ranar Litinin 8 ga watan Mayu ne mai martaba Sarki ya aika da kudin zuwa ga asibitin Aminu Kano da Nassarawa inda marar lafiyar yake jinya, kuma aka shirya komaai don ci gaba da bashi kulawar data dace.

Da yammacin ranar Talata 9 ga watan Mayu ne mai martaba Sarki yayi tattaki da kansa zuwa asibitin don duba mara lafiyar, kuma yayi masa addu'ar samun sauaki tare da fatan Allah ya tashi kafadunsa.

Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki

Sarki Muhammadu Sunusi dauke da Qur'anin da mara lafiyar ya bashi

Majiyar NAIJ.com ta shaida cewa marar lafiyar ya dauki Al-Qur'aninsa dayake karantawa ya mika ma mai martaba Sarki inda yace “Wannan ne abinda nake da shi kuma na baka.” Sarki kuma ya amsa yayi godiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai ya ya kamata a hukunta barayin gwamnati?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel