Manufofin Buhari sunyi dai-dai da namu – Kasar Amurka

Manufofin Buhari sunyi dai-dai da namu – Kasar Amurka

-Kasar Amurka ya bayyana fahimtar ta da Najeriya

-“Abinda sha’awa shine wannan manufa tashi tayi dai-dai da namu."

A jiya ne Talata, 10 ga watan Mayu, gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa manufofin da shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin cimma yayi daidai da nasu.

Mataimakin diraktan ofishin jakadar kasar Amurka akan harkokin Afrika ta yamma, Mr Nathan Holt, yayi wannan bayani ne a birnin Washington D.C.

Mr Nathan Holt yace : “A shekarar 2015, anyi wata zaben mai muhimmanci. An zabi Buhari a matsayin shugaban kasa."

“Wannan shine karo na farko a tarihin Najeriya inda akayi canjin mulki daga wata jam’iyya zuwa wata cikin zaman lafiya ba tare da zub da jini ba.

Manufofin Buhari sunyi dai-dai da namu – Kasar Amurka

Manufofin Buhari sunyi dai-dai da namu – Kasar Amurka

Wannan babban nasara ce ga Najeriya da Afrika gaba daya.

Manufan shugaba Buhari shine yaki da ta’addanci, musamman mayakan Boko Haram da wasu a yanin arewa maso gabas.

Yanada manufan bunkasa tattalin arzikin kasa, samar da aikin yi ga matasa, da kuma yaki da rashawa.

KU KARANTA: Abubuwa 3 da ke gaban Osinbajo

Abinda sha’awa shine wannan manufa tashi tayi dai-dai da namu.

Abinda nike nufi shine, wadannan manufofi sunyi daidai da manufar Amurka a Najeriya. Kuma muna son hada kai da Najeriya wajen yaki da rashawa."

“Mu kanmu muna son taimakawa masu hannun jari wajen kawo cigaba. Kuma muna goyon bayan yaki da rashawan shugaba Buhari,”.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel