Dansanda ya harbi budurwarsa, ya bindige kansa

Dansanda ya harbi budurwarsa, ya bindige kansa

- Jami'in dansanda ya harbe kansa bayan ya harbi budurwarsa a jihar Yobe

- Makwabtansa sun tabbatar da yawan samun rashin fahimta tsakaninsa da budurwar

Wani jami’in rundunar yansandan Najeriya ya bindige budurwarsa, sa’annan ya hallaka kansa a ranar Litinin 8 ga watan Mayu a garin Potiskum, na jihar Yobe.

A yanzu haka, budurwar na kwance a asibiti inda take jinyar harbin da dansandan yayi mata, wanda ya bar tad a munanan rauni.

KU KARANTA: Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:45 na safiyar ranar Litinin a dakinsa dake cikin tsohuwar sakatariya, a kusa da caji ofis na garin Potiskum.

Dansanda ya harbi budurwarsa, ya bindige kansa

Dansandan Najeriya

Kwamishinan yansandan jihar Yobe Abdulmalik Sunmonu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaida cewa dansandan na cikin dakin sa ne lokacin da aka jiyo karar harbi.

“Daga bisani sai aka gano dansandan ya harbi budurwarsa ne, sa’annan ya bindige kansa, daga nan sai aka garzaya dasu asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar dansandan, yayin da ita budurwae ke cikin mawuyacin hali.” Inji kwamishina Sunmonu.

Kwamishinan yansandan ya kara da cewa zasu cigaba da gudanar da bincike kan lamarin don gano yadda lamarin ya wakana.

Majiyar NAIJ.com ta zanta da wani makwabcin dansandan, wanda yace “Suna yawan samun rikici a tsakaninsu, dansandan na zargin budurwar tasa da cin amanarsa, amma ba’a taba tunanin zai aikata wannan ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jakadan zaman lafiyar Najeriya yayi magana, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

In da ranka, ka sha kallo: Yadda wani mutumi ya ƙulla kyakkyawar abota da Zakanya (Hotuna)

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel