Babu wanda ya tilasta ku sayen kamfanin wutar lantarki – Inji Fashola

Babu wanda ya tilasta ku sayen kamfanin wutar lantarki – Inji Fashola

- Fashola ya caccaki kamfanonin bada hasken wutar lantarki na kasa kan korafin rashin samu hadin kai mutane

- Ministan ya ce babu wanda ya tilasta su sayen kamfanin wutar lantarkin tun farko

- Kamfanonin sun koka cewa mafi yawan kayayyakin kamfanin hasken wutar lantarki sun tsufa

Ministan ayyuka da hasken wutar lantarki, Babatunde Fashola ya caccaki wadanda suka sayi kamfanin hasken wutar lantarki na kasa bayan sun koka kan rashin samun hadin kai daga masu amfani da hasken wutar lantarki.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, ministan ya ja hankalin wadannan kamfanoni wadanda a halin yanzu aka damkawa harkar wutar lantarki kan cewa har yanzu sun kasa zuba jari wajen inganta hasken wutar kamar yadda aka yi yarjejeniya da su kafin a yi masu gwamjon kamfanin.

KU KARANTA KUMA: Me yayi zafi? Soja da dukan Ɗansanda, Karanta

Game da koken da kamfanonin suka gabatatr kan cewa mafi yawan kayayyakin kamfanin hasken wutar lantarki sun tsufa, ministan ya kalubalance su kan cewa babu wanda ya tilasta su sayen kamfanin sannan kuma kafin su sayi kamfani sun rigaya sun san halin da yake ciki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyo inda wani ministan Buhari ya ce zuna hanyan suna aiki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel