Gwamnan Neja ya yabawa shugaba Buhari kan kubutar da 'yan matan Chibok

Gwamnan Neja ya yabawa shugaba Buhari kan kubutar da 'yan matan Chibok

- Gwamnan Jihar Neja ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kubutar da 'yan matan Chibok

- Gwamnan ya ce ya yabawa shugaban kan kyakkyawan manufar daukaka martabar kasar Najeriya

- Abubakar ya jinjinawa kokarin jami'an tsaron Najeriya ganin ansamu nasarar kubutar da 'yan matan Chibok

Gwamnan Jihar Neja Dakta Abubakar Sani Bello ya bayyana nasarar kubutar da 'yan mata 82 da Boko Haram ta sace a makarantar sakandare na garin Chibok a shekarar 2014 a matsayin wani gagarumin nasara ga shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnatin tarayya.

A wata takardar sanarwa da gwamnan ya fitar dake dauke da sa hannun sakataren yada laraban sa Malam Jibril Baba Ndace, gwamnan ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari a kan kokarin sa da jajircewar ganin an kubutar da wadannan 'yan matan sakantaren Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.

Gwamnan ya ce: “Shugaban kasa Buhari ya tabbatar wa duniya zai yi duk iya kokarinsa na ganin ya kubutar da wadannan 'yan mata da sauran wadanda suke hannun boko haram, tabbas mun fara ganin sakamakon hakan”.

KU KARANTA KUMA: Ana nema a tsige Buhari: Matasan APC sun gano makarkashiya

Gwamnan ya cigaba da cewar: “Shugaban kasa nada kyakkyawan manufar daukaka martabar wannan kasa, ina yimasa addu'ar Allah yakara masa lafiya da hazaka, ilimi da karfin guiwar ciyar da wannan kasa ta gaba”.

Gwamna Abubakar ya jinjinawa kokarin da jami'an tsaron Najeriya suka nuna musamman rundunar soji da sauran wadanda sukayi ruwa da tsaki dan ganin ansamu nasarar kubutar da wadannan 'yan mata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar lumana kan sace 'yan matan Chibok

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su
NAIJ.com
Mailfire view pixel