Rashin bayyana Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a wasikar Buhari ta janyo muhawara a zauren majalisar dattijai

Rashin bayyana Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a wasikar Buhari ta janyo muhawara a zauren majalisar dattijai

- Rashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a wasikarsa ta janyo muhawara a zauren majalisar dattijai

- Wasu ‘yan majalisa sun zargi shugaba Buhari da rashin fito fili wajen ambata Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa

A ranar Talata, 9 ga watan Mayu ne shugaban majalisar dattija sanata Bukola Saraki ya karantawa zauren majalisar wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika masu kan sake komawa birnin London domin a duba lafiyarsa.

Sai dai karanta wasikar ke da wuya muhawara ta barke tsakanin ‘yan majalisar, bisa abinda wasunsu suka kira da rashin bayyana mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da shugaba Buhari bai yi ba a matsayin mukaddashin shugaban kasa, a fayyace.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, cikin wasikar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ambata cewa babu kayyadajjen lokacin da zai dawo gida, dan haka mataimakinsa Farfesa Osinbajo zai cigaba da kula da al’amuran tafiyar da gwamnatin kasar, kamar yadda sashi na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada dama.

Rashin bayyana Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa a wasikar Buhari ta janyo muhawara a zauren majalisar dattijai

Zauren majalisar dattawan Najeriya

KU KARANTA KUMA: Abubuwa guda 5 da Osinbajo yayi tun bayan karbar ragamar mulki daga Buhari

Al’amarin da ya janyo kace-nace tsakanin wadanda ke ganin kamata ya yi a ce shugaban ya fito fili wajen ambata Farfesa Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Wasu masharhanta na kallon kalamin da shugaba Buhari yayi amfani da shi cikin wasikar a matsayin wanda bai kamata a ce ana ta cece kuce kansa ba, kasancewar kalamin na nuna cewa mataimakin nasa ne zai cigaba da jagorancin shugabancin kasar, har zuwa lokacin da zai dawo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel