An kammala aikin kasafin kudin bana kuma za a tabbatar a ranar Alhamis

An kammala aikin kasafin kudin bana kuma za a tabbatar a ranar Alhamis

- Kwamitin kasafin kudi a majalisar dattawa ta mika bayanan kudin kasafin kudin bana 2017 ga majalisar

- Shugaban majalisar ya yabawa kwamitin bisa kokarin da suka yi wajen sarrafa kundin kasafin kudin

- Shugaban ya ce zasu tabbatar da kasafin kudin na 2017 a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa sanata Danjuma Goje ya mika bayanan kundin kasafin kudin bana ga majalisa biyo bayan cece-kuce da al'ummar kasa suka yi tayi kan batun batar kasafin kudin bana a gidan sanata Danjuma Goje wanda hakan ya faru sakamakon samamen da 'yan sanda suka kai gidan sa.

Yanzu dai ta faru ta kare kundin kasafin kudin bana ya kammalu kuma tuni shugaban kwamitin kasafin kudi ya mika shi ga majalisa.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya yabawa kwamitin kasafin kudin bisa namijin kokarin da suka yi wajen sarrafa kundin kasafin kudin na bana daki-daki.

An kammala aikin kasafin kudin bana kuma za a tabbatar a ranar Alhamis

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa sanata Danjuma Goje ya mika bayanan kundin kasafin kudin bana ga majalisar

KU KARANTA KUMA: Osinbajo, Bukola da Dogara sunyi bankwana wa shugaba Buhari a tafiyarsa

Shugaban majalisar ya kuma jinjinawa kwamitin inda ya ce tun shekarar 1999 rabon majalisa da ta karbi daki-daki na bayanan kasafin kudi tare da kasafin kudin a lokaci guda.

Shugaban majalisar ya ce zasu tabbatar da kasafin kudin na 2017 a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kali yadda Buhari 2019 posters sun cika da ruwa tituna; ma farkon ko ma bad

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel