Wani masanin tsaro yayi Allah-wadai da PDP

Wani masanin tsaro yayi Allah-wadai da PDP

– An ceto ‘yan mata sama da 80 da aka sace lokacin tsohon shugaba Goodluck Jonathan

– Jam’iyyar PDP tace bai dace ayi musanya da ‘Yan ta’adda ba

– Sai dai Masana sun ce akwai rashin tunani a wannan maganar

Bangaren Ahmed Makarfi tace bai dace ayi musayar ‘yan Boko Haram da Matan Chibok ba.

Richard Murphy wani Masanin tsaro yayi tir da wannan magana.

Dama bangaren Ali Modu Sheriff sun yabawa Gwamnatin Najeriya.

Wani Masanin tsaro yayi Allah-wadai da PDP

'Yan matan nan na Chibok

Wani Masanin harkar tsaro a kasar Jamus Richard Murphy yayi Allah-wadai da abin da bangaren Ahmed Makarfi na Jam’iyyar PDP su ka fada game da ceto ‘Yan matan nan na Chibok. Murphy yace sai maras imani zai fadi wannan magana.

KU KARANTA: Matan Chibok: Abin da ya sa muka taimakawa Najeriya-Kasar Switzerland

Wani Masanin tsaro yayi Allah-wadai da PDP

'Yan matan Chibok: An yi Allah-wadai da PDP

Dayo Adeyeye na PDP yace akwai matsala wajen sakin ‘Yan ta’adda domin ceto wasu mata. Shi kuwa Masanin yace ko ‘Yan ta’adda 10 aka saki domin mace 1 ba a fadi ba ganin irin abin da zai kasance zai faru da ita idan aka yi sake.

NAIJ.com ta rahoto cewa Cairo Ojougba, wani Jagoran PDP a bangaren Ali Modu Sheriff ya yabawa shugaba Buhari da ceto ‘Yan matan Chibok. Ojougba ya bayyana cewa tsohon Shugaba Jonathan yayi kokarin dawo da matan gida amma abin ya faskara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za a raba Najeriya da gaske?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel