Shugaba Buhari ya nemi su Abba Kyari sauka daga matsayin su

Shugaba Buhari ya nemi su Abba Kyari sauka daga matsayin su

– A wata majiya Shugaba Buhari ya nemi Abba Kyari ya ajiye matsayin sa

– Haka-zalika kuma Ministocin sa irin su Fashola da Amaechi

– Ana zargin su da laifin sata a baya

Muna samun labari daga Jaridar Daily Post cewa shugaba Buhari ya nemi Abba Kyari ya ajiye aiki.

Haka kuma shugaban kasar yayi wannan kira ga Ministocin sa da ake zargi da laifi.

Yanzu haka dai shugaba Buhari ya bar kasar zuwa ganin Likita.

Shugaba Buhari ya nemi su Abba Kyari sauka daga matsayin su

Shugaban Ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari

NAIJ.com ta samu labari daga Jaridar Daily Post cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa Abba Kyari ya bar matsayin sa na shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa saboda zargin da ke kan sa na karbar cin hanci daga kamfanin MTN.

KU KARANTA: Rashin lafiya: Ana nema a tsige Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya nemi su Abba Kyari sauka daga matsayin su

Shugaba Buhari ya nemi Amaechi da Fashola su bar aiki

Akwai kuma jita-jitar cewa shugaban kasar ya fadawa Ministocin sa da ake zargi da sata lokacin su ke rike da wasu mukaman irin su Rotimi Amaechi da Babatunde Fashola su yi murabus. Sai dai mai magana da bakin shugaban kasar yace ba zai iya cewa komai ba don Buhari ba ya nan.

A farkon makon nan ne Mukaddashin shugaban Hukumar EFCC ya kai ziyarar Ofishin Hukumar na Yankin Jihar Ribas. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar yace sun yi na’am da aikin Magu na kokarin ganin bayan sata da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda ya kamata a hukunta barayin kasar nan

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel