Ana nema a tsige Buhari: Matasan APC sun gano makarkashiya

Ana nema a tsige Buhari: Matasan APC sun gano makarkashiya

– Akwai wata makarkashiyar sauke shugaban kasa Muhammadu Buhari

– Wata Kungiya ta Matasan APC ta bankado wannan shiri

– Shugaba Buhari dai ya koma Asibiti a can Birnin Landan

Wata Kungiya ta APC Youth Renaissance ta bankado wani shiri na sauke Shugaba Buhari.

Matasan su kace Sanatoci da wasu ne ke wannan yunkuri.

Shugaban kasar na fama da rashin lafiya.

Ana nema a tsige Buhari: Matasan APC sun gano makarkashiya

Sanatoci na da shirin tsige shugaba Buhari

Kamar yadda ku ka ji, NAIJ.com na samun labari daga wata jarida cewa wasu Sanatoci da manyan kasar na kokarin amfani da damar rashin lafiyar Muhammadu Buhari su sauke sa daga kujerar shugaban kasar.

KU KARANTA: Abubuwa 5 da Osinbajo ya karya da su

Ana nema a tsige Buhari: Matasan APC sun gano makarkashiya

Ana nema a sauke Buhari-APC Youth Renaissance

Sakataren Kungiyar Collins Edwin ya bayyana wannan, yace ba za su yarda da hakan ba inda yace a je-a dawo dai shugaba Buhari ya mika ragamar mulki hannun Farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ne Mataimakin sa. Sannan kuma yace ba tilas bane Buhari ya bayyana rashin lafiyar sa.

Jiya Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya karanta wasikar da shugaban kasa Buhari ya aiko zuwa ga Majalisar game da tafiyar sa zuwa Landan domin ganin Likita. Daga baya dai takardar ta jawo ce-ce-ku-ce.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Manyan labarai na wannan mako

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel