Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

-An yi gumurzu tsakanin jami'an hukumar kwastam da yan fasakauri a jihar Ogun

-An jikkata mutane da dama daga bangarorin hukumar kwastam da jami'an fasakaurin

Wasu jami’an hukumar kwastam reshen jihar Ogun sun yi musayar harsashi tsakaninsu da yan fasa kauri a ranar Talata 9 ga watan Mayu akan titin Ota-Idiroko.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar lamarin ya faru ne a lokacin da jami’an kwastam suka yi kokarin cafke wani sanannen dan fasa kauri mai suna Sheriff, a haka ne jami’an hukumar suka hallaka Sheriff a kan titin Ola na garin Ota-Idiroko yayin musayar harbe harben.

KU KARANTA: Abubuwa guda 5 da Osinbajo yayi tun bayan karbar ragamar mulki daga Buhari

Ana zargin Sheriff da abokan fasakaurinsa sun shigo da shinkafa, man gyada da sauran kayayyaki daga kasar Bini ta kan iyakar kasar da Najeriya, sai dai majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar Sheriff da abokansa suna baiwa jami’an Kwastam cin hanci ne domin su dinga shigo da kayayyakin.

Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri

Sai dai kisan Sheriff bai yi ma jama’an yankin dadi ba, hakan ya harzuka su suka shiga zanga zanga da kone kone, inda suka banka ma motar hukumar kwastam wuta, tare da jikkata wasu daga cikin jami’an hukumar.

Cikin wadanda aka jikkata har da jami’an yansanda da wasu jami’an hukumar sojin ruwa.

Da aka tuntubi Kaakakin hukumar Kwastam na jihar Ogun, Abdullahi Maiwada, yace rikicin ya samo asali ne lokacin da jami’a hukumar su suka tsare wasu masu sana’ar fasa kauri, daga nan ne suka far ma jami’an hukumar.

Jami’an hukumar hana fasa-ƙauri sun yi harbe harbe da masu fasa-ƙauri a Ogun

Motar jami’an hukumar hana fasa-ƙauri da aka kona

“Mun kama wata mota kirar Mazda mai lamba KTU 504 AN dauke da buhuna 45 na shinkafa, da wata motar Passat dauke da kwali 28 na man gyada, amma sai yan fasakaurin suka hada gangami suka kawo mana hari tare da kona mana mota” inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wasu hanyoyin tattala albashi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel