Ba zamu kara kudin albashi ba har sai mun biya basussukan da ke kasa – Gwamnatin tarayya

Ba zamu kara kudin albashi ba har sai mun biya basussukan da ke kasa – Gwamnatin tarayya

-Gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa kan al’amarin kara albashin ma’aikata

-Tace magana gaskiya shine gwamnati batada karfin yin hakan a yanzu

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ba zai yiwu ta kara kudin albashin ma’aikata ba har sai ta biya basussukan ma’aikatan da ke kasa yanzu.

Wannan na bayyana ne bayan ministan kwadago, Sanata Chris Ngige; ministan kudi, Kemi Adeosun; Diraktan ofishin kasafin kudi, Mr. Ben Akabueze; da shugaban kungiyar kwadado, Kwamred Ayuba Waba, suka gana da shugabannin majalisan dokokin tarayya akan yadda za’a biya basussukan ma’aikata da alawus.

Kana kuma da tattaunawa kan alwaus din wanda ya mutu yana bakin aiki.

Ba zamu kara kudin albashi ba har sai mun biya basussukan da ke kasa – Gwamnatin tarayya

Ba zamu kara kudin albashi ba har sai mun biya basussukan da ke kasa – Gwamnatin tarayya

Ngige ya bayyanawa manema labarai cewa sun zo majalisar ne bisa ga gayyatar shugabannin majalisar dokokin tarayya.

Ya kara da cewa suk da cewa an samu cigaba a ganawar, kowa zai koma gida sannan a dawo gobe da mafita kan al’amarin saboda gwamnati yanzu batada kudin dakile wadannan kalubale yanzu.

KU KARANTA: An bankado jabun taki a Zariya

Ngige yace : “Munzi ne bisa ga gayyatan majalisar dokoki domin wata ganawa da shugaban majalisan dattawa. Mun zo ne domin tattauna wasu abubuwa da suka shafi rashin zaman lafiya a wajen aiki.

Kamar yadda kuka sani kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa gwamnoni basu kla dasu yadda ya kamata.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel