‘Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa

‘Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa

-Fadar shugaban kasa tayi karin haske kan dalilin daya sa yan matan Chibok suka yi fes fes

-Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewar akwai bangarori da dama a kungiyar Boko Haram

Mashawarcin shugaban kasa ta fannin watsa labaru Femi Adesina ya bayyana dalilin daya sanya yan matan Chibok din da aka sako su 82 suka yi bul-bul tare da bayyana fes-fes ba kamar sauran da aka fara sakowa ba a watan Oktoban bara.

Adesina ya bayyana haka a wani shirin gidan talabijin na Channels mai suna ‘Sunrise Daily’ a ranar Litinin 8 ga watan Mayu, inda yace sai da aka shirya yan matan kafin aka kawo su fadar gwamnati domin ganawa da shugaban kasa, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan kishin al’umma sun gargaɗi gwamnatin Kano da masarautar Kano

Adesina ya kara bayanin cewar yanayin abincin da yan matan Chibok ke ci da walwalarsu ya danganta da bangaren dake rike dasu da kuma inda suke rike dasu.

‘Dalilin daya sa aka ga yan matan Chibok ɓul-ɓul’ – Fadar shugaban kasa

Adesina yayin hirar

“Kada ku manta, ba dukkanin matan bane suke rike a hannun bangare daya na Boko Haram, don haka walwalar su ta dangaanta da wadanda suke rike dasu, da kuma kulawar da suke basu.” Inji shi

Duk da cewa akwai bangarori da daman a kungiyar yan ta’addan, amma ba’a tabbatar da bangarori nawa bane.

Daga karshe Adesina ya tabbatar ma yan Najeriya gwamnati zata yi dukkanin kokarinta na ganin an sako sauran yan matan dake a hannun Boko Haram har zuwa yanzu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fastocin takarar Buhari sun fara yawo a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel