Jami’an yan sanda sun bankado buhun jabun taki akalla 1000 a Zaria

Jami’an yan sanda sun bankado buhun jabun taki akalla 1000 a Zaria

Ofishin hukumar yan sanda Zaria, jihar Kaduna, ta bankado kuma ta kwace sama da buhun taki jabu guda 1000 a wani masana’anta a Zaria.

Shugaban ofishin, ACP Abdullahi Ibrahim, ya bayyana wannan ne a wata hira da manema labarai yau a Zaria.

Masana’antan hada jabun takin na wani mutum Mohammed Lawal-Bashir, tana zaune ne a Dala Gwargwaje, Zaria.

Ibrahim ya kara da cewa bincike kan buhun taki daya ya nuna cewa an cudanya buhun taki daya da kasa domin samun buhun taki 6 jabu.

Jami’an yan sanda sun bankado buhun jabun taki akalla 1000 a Zaria

Jami’an yan sanda sun bankado buhun jabun taki akalla 1000 a Zaria

Game da cewarsa, an kai mai kamfanin da dukkan takin Kaduna domin bincike.

Da aka tuntubi shugaban kungiyar dilolin takin Zariya, Alhaji Sani Danmarke, ya nisantar da kanshi daga wannan aika-aika.

KU KARANTA: Wani soja ta nushi dan sanda a gaban gwamna

Yace kungiyar ta nada kwamitin tsaro wanda zai dinga yawo domin bankado azzalumai cikin yan kasuwan. 

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel