Shettima da manyan mutanen garin Chibok Sun godewa Buhari da Osinbajo bayan ceto yan mata 82

Shettima da manyan mutanen garin Chibok Sun godewa Buhari da Osinbajo bayan ceto yan mata 82

- Tawagar da gwamnan ya jagoranta sun kunshi yan majalisa masu wakiltar jihar Borno, shuwagabannin Chibok, da kuma manyan dattijan unguwanni kari akan gwamnonin Akwa Ibom da Zamfara

- Osinbajo shine ya tare su a yayinda yake a matsayin shugaban rikon kwarya a gurbin shugaban kasa da ya tafi Landan don kiwatar lafiyarsa

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya jagoranci tawagar ne izuwa Aso Rock a ranar litinin domin godiya wa Shugaba Muhammadu Buhari a dacen da akayi na yanto yan matan makaranta guda 82 daga hannun miyagu tsawon shekaru uku.

Tawagar ta kunshi dukkanin yan majalisar jihar Borno, da wakilan Jihar a majalisar dattijai, da shuwagabannin Chibok sannan da gwamnonin Akwa ibom da Zamfara.

Wanda ya taresu shine a yayinda yake a matsayin shugaban rikon kwarya a gurbin shugaban da yake Landan don kiwatar lafiyarsa.

‎Tattareda farinci NAIJ.com ta rawaito cewa gwamnan bornon yace: ''Bamusan wanne zamu godewa ba, shin yanto yaran 82, ko yanto 21 na karon farko da jagorancin yayi mana.''

KU KARANTA: An kashe wani fitinarnen dan fashi da makami a Zamfara

Yace girman ka ya karu, kimanin shekaru 100 baya wata mawallafiyar littafi a Amurka yayi rubutu mai ban kaye gameda godiya tace, godiya a zuci baya isuwa kuma baya wadatarwa ballantana yakaiga wanda akeyiwa ba tareda furuci ba.

Zuwanmu nan munzo ne don Nuna godiyarmu ba a zuci kadai ba, Harma a gabbai gameda kyautatawa da cika alkawarin da wannan gwamnatin, sojoji, jami'an tsaro da mashawartan sukayi mana a kokarin dawo mana da y'ay'anmu.

Mr. Shettima ya kara da cewa, “muna kara amfani da wannan damar don mika godiya wa Gwamnatin Swizaland ta hanyar bijimin kokarin da sukayi mana da taimakon Kungiyar Redikros

''Mun jinjinawa Shugaba Buhari a bibitarsa gun tabbatarda dawowar yaran.''

NAIJ.com ta nakalto cewa Gwamnan Jihar Borno yace a mahangarsa Shugaba buhari babu shakka yayi nasara a samarwa da Najeriya samun karbuwa a mu'amalolinta da Sauran kasashen duniya. Kuma ina tabbatarda cewa Shugaban zaici nasara a kawo karshen Boko Haram.

A karshe ya yabi kokarin mataimakin shugaban kasa Osinbajo a taimakonsa da yake bayarwa a cigaban ayyuka a Rikon kwaryar da yake yi.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota
NAIJ.com
Mailfire view pixel