Yan kishin al’umma sun gargaɗi gwamnatin Kano da masarautar Kano

Yan kishin al’umma sun gargaɗi gwamnatin Kano da masarautar Kano

-Wasu kungiyoyin cigaban jihar Kano sun ja hankalin gwamnati da fadar shugaban kasa

-An sabani tsakanin banagrorin ne tun bayan rikicin badaklar almubazzaranci

Gamayyar kungiyoyi masu kishin al'umma a Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya sun bukaci gwamnatin jihar da kuma masaurtar Kano da su yi hattara da irin mutanen da ke kokarin amfani da sabaninsu wajen ruruta wutar rikici a fadin jihar.

Gamayyar kungiyoyin sun kuma ja hankulan bangarorin biyu kan mummunan sakamakon da al'ummar jihar za su fuskanta sanadiyyar rikicin wanda wasu ke aiki ta karkashin kasa domin ganin cewar ba a kai ga warware sabanin ba.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun yi raddi ga addu’ar Fani Kayode ga Buhari

Gidan rediyon BBC Hausa ta ruwaito kungiyoyin sun ce zasu ci gaba da aiki tare da dukkanin masu ruwa da tsaki a lamarin domin ganin sulhu tsakin bangarorin biyu ya dore don kawar da barazanar tsaro.

Yan kishin al’umma sun gargaɗi gwamnatin Kano da masarautar Kano

Masarautar Kano

Kaakakin gamayyar kungiyoyin Kwamared AbdulMajid Sa'ad ya bayyana ma manjiyar NAIJ.com cewar ya kamata a samu fahimtar juna tsakanin bangaren gwamnati da masarauta don a kawar da duk wani barazana ga zaman lafiya a jihar Kano.

Ana ganin binciken da hukumar sauraren korafin jama'a da kuma yaki da cin hanci ta Kano keyi a masarautar jihar bisa zargin barnatar da makuden kudade ba bisa ka'ida ba shine abin da ya samar da sabani tsakanin gwamnatin jihar da kuma Masarautar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarkin Kano yayi baran bantama

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel