Me yayi zafi? Soja da dukan Ɗansanda, Karanta

Me yayi zafi? Soja da dukan Ɗansanda, Karanta

-Babban soja ya dankara ma kwamishinan yansandan gula a ido

-A yanzu haka kwamishinan yansandan yana jinya a asibitin jihar Kaduna

An kwantar da kwamishinan yansandan jihar Borno Damian Chukwu bayan ya sha gula a ido a hannun wani babban soja mai mukamin kanal a lokacin dayake kokarin sara ma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Wannan lamari ya faru ne a gidan gwamnatin jihar Borno, hakan ya sanya kwamishinan jinya a wani asibiti dake jihar Kaduna, sakamakon zafin gulan da sojan yayi masa.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun yi raddi ga addu’ar Fani Kayode ga Buhari

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar “Hafsoshin yansandan jihar Borno na cikin bacin rai sakamakon faruwar lamarin.”

Me yayi zafi? Soja da dukan Ɗansanda, Karanta

Kwamishina Damin Chukwu

Majiyar ta cigaba “Kwamishinan na kusa da sojan ne a lokacin da sojan ke kokarin sara ma gwamna Kashim Shetima ne, tsautsayi ya sa hannunsa ya dake kan idonsa na hannun dama, nan da idon kwamishinan ya kumbura.”

Daga karshe, majiyar ta bayyana cewar kwanaki bakwai kenan kwamishinan na fama da jinya a garin Kaduna, amma ya fara samun sauki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin Boko Haram a jihar Borno

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel