Kwararren likitan Dabi'a ya bada shawarar a yiwa yan matan Chibok gwajin yanayin dabi'unsu

Kwararren likitan Dabi'a ya bada shawarar a yiwa yan matan Chibok gwajin yanayin dabi'unsu

- Ajiboye ya kara da cewa tashin-tashinar da yaran suka fuskanta na iya haifarda matsalolin rashin lafiyan kwakwalwa kamar rikicewa, firgici, kasa gane mutane,damuwa da mantuwa

- Gwajin zai kunshi harda tambayoyi tareda lura da amsoshin da zasu bayar a dabi'ance a yayin bayar da magunguna a garesu

Mr Adedotun Ajiboye, babban likitan ilimin dabi'a a bangaren yankin a asibitin koyarwa dake jihar Ekiti ya bada shawarar a binciki yanayin dabi'ar yan matan nan 82 da aka fanso don samun tabbaci gameda kyautatuwar lafiyarsu.

Ajiboye a cewar NAIJ.com ya bada shawarar ne a tattaunawar da akyi dashi ta wayar tangaraho da manema labarai ranar Litinin a Abuja.

A yawun maganarsa, gwajin zai kunshi tambayoyi tareda lura da amsoshin da zasu bayar a dabi'ance a yayin bayar da magunguna a garesu.

Ajiboye ya kara da cewa tashin-tashinar da yaran suka fuskanta na iya haifarda matsalolin rashin lafiyan kwakwalwa kamar rikicewa, firgici, kasa gane mutane,damuwa da mantuwa.

KU KARANTA: Dalilin da kotu ta umarci sufeto-janar na 'yan sanda ya biya maza 4 miliyan N1 kowane

“A bisa yanayin banbancin mutane, fuskantar tashin hankalin da sukayi na iya banbanta bisaga ga yanayin halittarsu, illar na iya fin shafar wasu sama da wasu.''

Haka kuma rashin lafiyar da ke iya samun su ma na iya bambanta, shiyasa akwai bukatar gwaji gameda hakan.

NAIJ.com ta nakalto cewa daga ire-iren gwajin da za'ayi akwai; chemotherapy-biological, psychotherapy-psychological, family therapy and stress management. sannan renon wayar dasu , tabbatardasu da kuma dawoda yanayin tunanurnukansu ingantarce.

Yace akwai bukatar tallafi daga manyan kasa don kyautatuwar yaran,sannan gwamnati,sojoji da likitoci da sauran jama'a dasu kyautata mu'amalantar su ga yaran.

“bugu da kari yanayin lura da gwaje-gwajen bai kamata ya zama akan gaggawa ba lura da halin da yaran suka tsinci kansu.kungiyar redkross ta duniya ta mika yaran guda 82 wa shugaba buhari kafin tafiyarsa Ingila.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel