Daga karshe, Majalisar dokokin tarayya zata bayyana kasafin kudinta

Daga karshe, Majalisar dokokin tarayya zata bayyana kasafin kudinta

-Majalisar dattawa ta ji kukan yan Najeriya akan kasafin kudin su

-Tace zata bayanna yanzu bayan shekaru 8

Shugabannin majalisar dokokin tarayya ta amince da bayyana kasafin kudinta na 2017 ga jama’a bayan sun ki amincewa shekaru 8 da suka wuce.

Sun yanke wannan shawara ne a wata ganawar shugabannin majalisar dattawa da na majalisar wakilai wanda sukayi da dare a gidan shugaban majalisan Bukola Saraki da ke Maitama Abuja.

Bisaga wannan shawara, za’a gabatar da kasafin kudin 2017 a majalisa yau Talata domin tabbatar da shi.

Daga karshe, Majalisar dokokin tarayya zata bayyana kasafin kudinta

Daga karshe, Majalisar dokokin tarayya zata bayyana kasafin kudinta

“Yanzu an tabbatar, za’a gabatar da kasafin kudin 2017 da safen nan. Majalisar dattawa da wakilai sun amince da hakan,”.

Majiyar bata bayyana yawan yawan kasafin kudin. A makon da ya gabata, Saraki ya bayyana cewa zai cika alkawarinsa da bayyana kasafin kudin 2017.

KU KARANTA: An damke mutane 18 a jihar KAduna

Saraki wanda yak i cika alkawarinsa akalla sau 6 kenan, amma mai magana da yawunsa, Bankole Omishore, yayi alwashi yin murabus idan Saraki bai cika alkawarinsa ba.

Mr. Omisore yace sai da akayi shekaru 2 kafin majalisan dokokin su yarda a bayyana kasafin kudin majalisar.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel