Har yanzu akwai sauran yan matan Chibok 114 a hannun Boko Haram

Har yanzu akwai sauran yan matan Chibok 114 a hannun Boko Haram

-Sauran yan matan Chibok a hannun Boko Haram sun kai 114

-Gwamnati ta fara yarjejeniya da yan Boko Haram domin cetto sauran yan matan

Jaridar Daily Trust ta samo wano sahihin rahoto daga majiya mai tushe na cewar gwamnati ta fara sabon tattaunawa da yayan kungiyar Boko Haram don ganin an sako sauran yan matan Chibok su 114 dake hannunsu har yanzu.

Majiyar ta shaida mana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a cigaba da tattaunawa don ganin an sako sauran matan, “Amma a gaskiya wasu daga cikinsu basu son dawowa, kun san mun fada muku cewar a cikin guda 21 da aka sako a watan Oktoba sun bayyana cewar dayawa daag cikin kawayensu basu son dawowa.” Inji majiyar

KU KARANTA: Fargaba a Borno kan musayar 'yan matan Chibok

Majiyar ta cigaba da bayyana cewar, daya daga cikin sharuddan da Boko Haram ta sanya shine ba zata tilasta ma kowacce yarinya dawowa ba, kamar yadda basu tilasta musu barin addininsu ba.

Har yanzu akwai sauran yan matan Chibok 114 a hannun Boko Haram

Yan matan Chibok

“Kun san cewa wasu daga cikin yan matan sun mutu sakamakon yaki, wasu kuma sun mutu ne sakamakon rashin lafiya, don haka ba lallai bane a same su gaba daya.” inji majiyar

Dama dai NAIJ.com ta ruwaito muku cewar wasu daga cikin yan matan basu da niyyar dawowa sakamakon sun aure wasu kwamandojin Boko Haram, yayin da wasu kuma suna da yara dasu.

Idan ba’a manta ba, a ranar 14 ga watan Afrilu ne Boko Haram ta saci yan mata 276 daga makarantar yan mata na garin Chibok, inda 57 daga cikinsu suka tsere yayin da suke kan hanyar shiga dajin Sambisa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyayen yan matan Chibok sun koka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel