Majalisar Dinkin Duniya ta yi murna da kubutar da ‘yan matan Chibok

Majalisar Dinkin Duniya ta yi murna da kubutar da ‘yan matan Chibok

- Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa kokarin gwamnatin Najeriya yadda ta kubutar da ‘yan matan makarantar Chibok 82

- Hukumar ta shawarci ‘yan Najeriya da su rike ‘yan matan da hannu biyu, kuma a basu taimako da suke bukata

Majalisar Dinkin Duniya MDD ta ce tana marhaban da kubutar da yan mata 82 na makarantar Chibok da yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Najeriya, kuma ta yi kira ga iyalai da jama’a da a taimakawa wadannan yan mata da suke cikin damuwa.

kakakin sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres aranar Litinin, 8 ga watan Mayu ya ce hukumar na kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su rike ‘yan matan da hannu biyu, kuma a basu taimako da suke bukata don su ci gaba da rayuwarsu tare da jama’a.

Kakakin Stephane Dujarric ya ce ana yin watsi da yan mata da aka taba yi musu fyade a cikin al’umma.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi murna da kubutar da ‘yan matan Chibok

Kungiyar nuna goyon bayan dawo da 'yan matan Chibok

KU KARANTA KUMA: Za'a sake sako wasu karin yan matan Chibok nan ba da dadewa ba - Minista

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alkawarin sa ido da kansa a kan kyautata rayuwar ‘yan matan da aka kubutar dasu.

Gidauniyar kula da yawan al’umma ta MDD ta aika da rukunin masana a Najeriya ciki har da masu nasiha da likitoci da zasu taimakawa ‘yan matan su ci gaba da rayuwarsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar tunawa da 'yan matan Chibok bayan shekaru 3

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel