Najeriya ta fi kowani kasa yawan hadarin mota a Afrika - FRSC

Najeriya ta fi kowani kasa yawan hadarin mota a Afrika - FRSC

Hukumar tsaron hanyoyin motan tarayya, FRSC, tayi lissafin cewa cikin kowani mutane 100,000 a Najeriya, mutane kusan 40 ke mutuwa sanadiyar hadarin mota kowani shekara.

Shugaban hukumar FRSC ta kasa, Boboye Oyeyemi, ya bayyana hakan ne a wata taron kaddamar da shirin tsaron hanyar duniya a sakatariyan NUJ a Kaduna.

Wanda ya wakilce sa a taron, Yomi Asaniyan, Boboye Oyeyemi yace game da cewar kungiyar lafiyan duniya WHO, akalla motoci 7.6 million ne ke hawan titunan Najeriya.

Game da cewarsa, lissafin ya nuna cewa nauyi yayi yawa akan hanyoyi shi yasa hadura ke yawa a kasan.

Najeriya ta fi kowani kasa yawan hadarin mota a Afrika - FRSC

Najeriya ta fi kowani kasa yawan hadarin mota a Afrika - FRSC

" Hukumar FRSC a kokarinta ta gabatar da na’urar rage gudun mota motocin haya kuma tana bibiyan masu biyayya ko sabawa.”

Yace kashi 33 cikin 100 sukayi biyayya kan wannan umurni zuwa yanzu.

KU KARANTA: An damke mutane 18 game da rikicin jihar Kaduna

“Kasashen da suka samu nasarar rage haduran titin mota sunyi hakane wajen gabatar da tsarii ta hanyar rage gudun mota da kuma ilmantar da mutane kan hadarin gudu a mota.

” Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan aiwatar wajibcin sanyar na’urar a watan Oktoba, 2016.”

“Mun yanke wannan shawara ne akan lissafin da muka samu na fadin kasa ya nuna cewa gudu da mota ummul haba’isin kashi 60 cikin 100 na haduran Najeriya.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel