An damke mutane 18 game da rikicin da ya faru a jihar Kaduna

An damke mutane 18 game da rikicin da ya faru a jihar Kaduna

-A jiya da safe, an samu wata tashin hankali a jihar Kaduna

-An samu rahoton cewa mutane 3 sun rasa rayukansu a rikicin

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki wani jawabi inda yace jami’an tsaro sun garkame wasu yan barandan sa suka tayar da zaune tsaye jiya 9 ga watan Mayu a jihar Kaduna.

Jami’an tsaro sunyi ram mutane 18 wadanda ake zargin su suka tayar da kuran rikici tsakanin mazauna Kabala West da Ungwan Muazu, kuma za’a gurfanar da su a kotu.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki wani jawabi inda yace jami’an tsaro sun garkame wasu yan barandan sa suka tayar da zaune tsaye jiya 9 ga watan Mayu a jihar Kaduna.

An damke mutane 18 game da rikicin da ya faru a jihar Kaduna

An damke mutane 18 game da rikicin da ya faru a jihar Kaduna

Jawabin ta karyata maganganun kafafen yada labarai cewa rikicin ya shafi wasu sassan jihar Kaduna kuma wai an hallaka mutane da jikkata wasu.

Mr. Aruwan ya kara da cewa gwamnatin jihar ta tura wakilai domin sulhu tsakanin mazauna Kabala da Unguwan Muazu.

KU KARANTA: Yakubu Dogara yayi magana a sarakunan gargajiya

Wakilan sun kunshi sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Ibrahim Sani; mai baiwa gwamna shawara kan tsaron gida, da Aruwan kuma sun gana da shugabannin kungiyar CAN, Jama’atu Nasril Islam (JNI), kungiyoyin matasa, jami’an tsaro da sarakunan gargajiya.

“A karshen ganawar, bangarorin biyu sun amince da cewa za’a fito da duk wadanda ke da hannu a cikin rikicin domin fuskantar hukuma”.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel