Dalilin da kotu ta umarci sufeto-janar na 'yan sanda ya biya maza 4 miliyan N1 kowane

Dalilin da kotu ta umarci sufeto-janar na 'yan sanda ya biya maza 4 miliyan N1 kowane

- Hukumar ‘yan sanda ta ci gaba da tsare masu kara a gidan yari

- Hukuncin zama ya kare da kwana 14, amma hukumar ‘yan sanda basu karbi wani sabo

- Wani Sufeto Tony Alabi ya kama masu karan a ranar 17 ga watan Disamba shekara 2015

- A ranar karewan umurnin, babu sabuntawa da aka sanya har Afrilu 5

Babban kotu dake zaune a Maitama Abuja jiya ta ba Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris umarnin ya biya miliyan N1 wa kowane maza 4 don take hakkin dan Adam.

Mazan, Ozor Okolocha, Elvis Obiaku, Edward Onyenoknone da Imoni Mika sun kai kara na IGP da kuma kwamishinan 'yan sanda babban birnin tarayya Abuja zuwa kotu.

Alkali, Jude Okeke a cikin shari'a ya gudanar da cewa hukumar ‘yan sanda ta ci gaba da tsare masu kara a gidan yarin Keffi, ba tare da kotu ta yanke musu hukuncin zama. Alkali ya ce hukuncin zama ya kare da kwana 14, amma hukumar ‘yan sanda basu karbi wani sabo bayan da wani da sun karba ya kare. Ya ce kuma ‘yan sanda basu caje su ba.

Babban kotu dake zaune a Maitama Abuja jiya ta ba Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris umarnin ya biya miliyan N1 wa kowane maza 4 don take hakkin dan Adam

Babban kotu dake zaune a Maitama Abuja jiya ta ba Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP), Ibrahim Idris umarnin ya biya miliyan N1 wa kowane maza 4 don take hakkin dan Adam

KU KARANTA: Wacce rawa Osinbajo zai taka a karo na biyu a matsayin muƙaddashi?

Alkali ya ce: "Wannan babban take hakkinsu ne kamar yadda aka samar da tanade-tanaden sashe 35 na kundin tsarin mulkin 1999 na tarayyar Najeriya a matsayin an gyara.

"Kamar diyya na take musu hakkinsu, miliyan N 1 ya kamata a biya kowane daga cikin masu kara don wahala da kuma kunya da suka sha."

Alkali Okeke ya kuma gudanar da cewa wakafi na masu kara da kuma take hakkin 'yancinsu bai barata bisa tanade-tanaden na cikin Dokar shari'a' na Aikata Laifuka (ACJA), 2015.

Ya kuma bada umurni cewa kar ‘yan sanda su sake kama su a kan al'amurra da suka shafi maganan.

KU KARANTA: Najeriya na kashe kimanin $1bn a yawon kiwon lafiyar Shugaba Buhari da wasu – Minista

NAIJ.com ya tara cewa, wani Sufeto Tony Alabi ya kama masu karan a ranar 17 ga watan Disamba shekara 2015 da kuma ranar 6 ga watan Janairu, 2016 a garinsu Ase-Omuku a karamar hukumar Ndokwa Gabas jihar Delta ya kuma kawo su Abuja. Sa'an nan aka tsare su a kurkuku na karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa a kan hukuncin zama a gidan yari daga kotun majistare dake Abuja.

Duk da haka, a ranar karewan umurnin, babu sabuntawa da aka sanya har Afrilu 5, lokacin da aka yi cajin na take hakkin da muhimman hakkokin yan-adam kafin babban kotun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com bidiyo na gabatar da mace mai aikin gyaran mota

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel