Wacce rawa Osinbajo zai taka a karo na biyu a matsayin muƙaddashi?

Wacce rawa Osinbajo zai taka a karo na biyu a matsayin muƙaddashi?

- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake tafiya birnin Landon don a sake duba lafiyarsa inda mataimakin shugaban kasa ne zai ci gaba da jan ragamar kasar

-hugaba Buhari ya ce za a ci gaba da tafiyar da al'amuran gwamnati kamar yada aka saba, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa

A karo na biyu a cikin wannan shekarar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sake tafiya birnin Landon don a sake duba lafiyarsa.

Dama dai yanayin lafiyarsa ya zama wani babban abin damuwa a kasar, inda ake cike da tsoron samun gibi a wajen jagorancin kasar zai iya shafar farfadowarta daga matsin tattalin arzikin da take fuskanta.

Amma a cikin sakon da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ya ce, ka da 'yan kasar su tayar da hankalinsu.

Wacce rawa Osinbajo zai taka a karo na biyu a matsayin muƙaddashi?

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo kafin tafiyarsa a ranar Lahadi zuwa Landon

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kafin shugaba Buhari ya bar kasar ya gana da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, sanata Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara. Haka kuma sai da aka aika wasika zuwa majalisar dokokin kasar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Sashe na 145 (1) na Kundin tsarin mulkin ya ce, "A duk lokacin da shugaban kasa ya aika wa shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai wasika cewa zai tafi hutu ko kuma wani dalili zai sa ba zai iya zuwa ofis ba, to mataimakin shugaban kasa ne zai ci gaba da jan ragamar kasar, har sai lokacin da shugaban da kansa ya sake aika wata wasikar da zai bukaci a janye hakan."

'Yan Najeriya suna nuna matukar damuwa kan rashin lafiyar shugaban bisa fargabar kada a maimaita irin abin da ya faru a shekarar 2009 a lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'adua ya yi ta fama da rashin lafiya, al'amarin da har ya sa aka kai shi kasashen Saudiyya da Jamus don neman magani.

KU KARANTA KUMA: Babu wani dar-dar da ake yi a Najeriya-Inji Fadar shugaban kasa

Kuma saboda bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ba da kuma rashin bayyanawa 'yan kasar halin da yake ciki hakan ya jawo cece-kuce sosai a kasar. Shugaba 'Yar adua ya rasu a watan Mayun 2010 a sanadiyyar rashin lafiyar.

Sai dai a nasa bangaren a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu da daddare, shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, kamar dai yadda ya yi lokacin da ya tafi hutun jinya a watan Janairu, inda ya shafe tsawon mako bakwai.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Lahadi kan tafiyar tasa ba ta fadi tsawon lokacin da zai shafe a Landon din ba, "Likitoci ne za su fadi iya lokacin da zai shafe a can."

Amma ta kara da cewa, "Za a ci gaba da tafiyar da al'amuran gwamnati kamar yada aka saba, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa."

A wancan lokaci dai Mista Osinbajo ya samu yabo ta bangarori da dama saboda 'yadda ya tafiyar da mulkin kasar' a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasa.

Matakan da Osinbajo ya dauka na gaggawa wurin tunkarar matsalolin da kasar ke fuskanta bayan tafiyar Shugaba Buhari hutun jinyar na farko, sun bai wa masu sharhi mamaki.

Kuma hakan ya sa wasu ke ganin ya yi wa mai gidan nasa zarra a wata dayan da ya shafe yana lura da al'amuran kasar.

KU KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar cewa, kwamitin Osinbajo kila ya bada rahoto a kan al’amarin Babacir/Oke - Shugabanci

Sai dai fadar gwamnatin kasar ta ce duk wani yunkuri na nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari "kokari ne na kawo rudani".

Duk da tsokacin da fadar shugaban kasar ta yi kan wannan batu, bai sa wasu 'yan kasar sun yi shiru ba, musamman game da matakin da babban bankin kasar CBN ya dauka na rage farashin dalar Amurkar da yake sayar wa mutane daga N375 zuwa N360.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Koma bayan tattalin arziki ba laifin gwamnati ba ne, inji yan kasuwa a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel