Najeriya na kashe kimanin $1bn a yawon kiwon lafiyar Buhari, da wasu –Minista

Najeriya na kashe kimanin $1bn a yawon kiwon lafiyar Buhari, da wasu –Minista

- Yawon kiwon lafiyar da sauransu da yan Najeriya keyi a kasashen waje na daga abinda ke jawo zagon kasa wa tattalin arzikin Najeriya

- Gwamnatin kasa har yanzu bata bayyana takamaiman abinda ke damun shugaban ba da kiyascin kudin da ake kashewa a kiwon lafiyar tasa

Ministan kiwon lafiya, Dr. Osagie Ehanire ya bayyanar a ranar litinin cewa yawon kiwon lafiyar da yan Najeriya keyi a kasashen waje na daga abinda ke jawo zagon kasa wa tattalin arzikin Najeriya.

Ya nuna hakan ne a cewar NAIJ.com ta hanyar bibitar lissafin kidirdiga yawan yan najeriya dake fita don neman waraka kasashen waje na sa Najeriya kahse kudi kimanin dalar Amurka biliyan daya a shekara .

Ehanire yayi wannan furucin daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dade da barin kasar ba Zuwa Landan don manufa kwatankwaciyar haka.

Tundaga Hawan shugaban kawowar yanzu,yayi tafiye-tafiye don kiwatar lafiyarsa izuwa kasashen waje.

KU KARANTA: Ba gazawa bane fitar Shugaba Buhari domin lura da lafiyarsa - Imam

Kafin zuwansa Landan kiwatar lafiyarsa ya yi kwanaki a hutunsa arba'in da tara a United Kingdom.

Gwamnatin kasa har yanzu bata bayyana takamaiman abinda ke damun shugaban ba da kiyascin kudin da ake kashewa a kiwon lafiyar tasa.

Ehanire, a jawabinsa a bude bangaren lura da cuturtukan zuciya a asibitin Reddington Legas,yace tafiye tafiyen yan najeriya nasa Najeriya hasarar kudi dala biliyan daya $1b a shekara kuma hakan na daga dalilan dake kara talauta kasar.

ya nuna cewa dukda wani lokacin rashin kayan aiki da kwararrun likitoci na bada damar hakan,akwai da dama daga asibitoci masu zaman kansu dake kokari matuka kuma kamata yayi gwamnati tayi wani abu akan hakan don kara karfafansu ta hanyar karfafan itama hukumar lura da lafiya ta kasa baki daya. yin hakan zai kara yawan kudin shiga da kuma kusanto da nesa kusa wa masu larurorin dake fita wajen najeriya ta hanyar ba sai sun bukaci kashe kudin passport ba ko jirgin sama.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel