Za'a yi dokar gwajin kanjamau kafin aure a jihar Kano

Za'a yi dokar gwajin kanjamau kafin aure a jihar Kano

- Hukumar yaki da cutar AIDS ko Sida ta jihar Kano ta ce tana neman majalisar dokokin jihar ta wajabta gwajin cutar

- Ta ce kiddiga da aka gudanar a bara ta nuna cewa kimanin kashi biyu bisa dari na mutanen da ke jihar na dauke da cutar

- Shugaban hukumar ya ce yin dokar zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar tsakanin ma'urata a jihar

Hukumar da ke yaki da cutar AIDS ko Sida ta jihar Kano, na neman majalisar dokokin jihar ta wajabta gwajin cutar kafin ayi aure.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari cewa, hukumar ta bayyana cewa wata kiddiga da aka gudanar a bara ta nuna cewa kimanin kashi biyu bisa dari na mutanen da ke jihar na dauke da cutar ta Sida.

KU KARANTA KUMA: Mai aiki ta sanya guba cikin abincin maigidanta

Sai dai hukumar ta ce duk da wannan kididdiga, adadin mutanen da ke kamuwa da cutar na raguwa a jihar.

Za'a yi dokar gwajin kanjamau kafin aure a jihar Kano

Hukumar ta ce yin gwajin cutar Sida zai taimaka wajen hana yaduwarta

Shugaban hukumar Dakta Usman Bashir ya shaida ya ce, yin dokar zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar tsakanin ma'urata a jihar.

Ya kara da cewa, hukumar ta na fadakar da jama'a a makarantu da sauran wurare kan yadda za su kaucewa kamuwa da cutar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sariki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari a cikin wannan bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel