Akwai yiwuwar cewa, kwamitin Osinbajo kila ya bada rahoto a kan al’amarin Babacir/Oke - Shugabanci

Akwai yiwuwar cewa, kwamitin Osinbajo kila ya bada rahoto a kan al’amarin Babacir/Oke - Shugabanci

- Fadar Shugaba ta tabbattar Shugaban kasar Buhari zai karbi rahoton yau

- Yemi Osinbajo jiya ya gana da Buhari kafin ya yi tafiya zuwa Landan

- Zai yiwuwar mataimakin Shugaba ya bada rahoton a lokacin ganawar

- 'Yan Najeriya su jira “adalci," daga rahoton

Fadar Shugaban kasar na cewa kwamiti da ya yi diddigin zargi na Sakataren Gwamnatin Tarayya da aka dakatar da, Babachir Lawal da kuma Darektan-Janar na Hukumar Leken Asiri, Ayo Oke, da yiwuwar ya bayar da rahoto ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Musamman mai shawara ga Shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Mista Femi Adesina, ya fada jiya, yayin da ya fita a kan shirin Talabijin ‘Channels’.

KU KARANTA: Burin mu muyi fito-na-fito da Buhari a zaben 2019 — Inji PDP

NAIJ.com ya ruwaito cewa, an yi binciken Babachir ga zargin take hakki na doka da kuma tsari na bada kwangila a karkashin dabara na shugaban kasa a kan Arewa maso Gabas. Oke kuma, a kan miliyan $43, da hukumar EFCC suka gano a wani gida; hasumiya Osborne, Ikoyi, Legas.

Fadar Shugaban a ranar Laraba da ta gabata ta tabbattar cewa Shugaban kasar Buhari zai karbi rahoton yau.

Mataimakin Shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya gangarawa kwamiti na mutane 3 a kan zargin Babacir Lawal

Mataimakin Shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya gangarawa kwamiti na mutane 3 a kan zargin Babacir Lawal

Amma Mista Adesina jiya na cewa, mataimakin Shugaban kasar Yemi Osinbajo, wanda ya gangarawa kwamiti na mutane 3, jiya ya gana da Buhari kafin ya yi tafiya zuwa Landan don kiwon lafiyarsa.

KU KARANTA: Fargaba a Borno kan musayar 'yan matan Chibok

Mai magana da yawun Shugaban ya bayyana cewa zai yiwuwar mataimakin Shugaba ya bada rahoton a lokacin ganawar. "Mataimakin shugaban kasar ya gana da shugaban kasa jiya kafin ya yi tafiya. Yana yiwuwar ya bada rahoton a lokacin,"Adesina ya ce.

Ya kuma bayyana cewa irin halin 'yan kwamitin, ya kamata 'yan Najeriya su jira “adalci," daga rahoton.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan NAIJ.com na tambaya yarda ya kamata a hukunta jami'in masu cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel