Kotu taki sauraron rokon da Patience Jonathan tayi na kar a rufe ma'ajiyanta na $15.591m

Kotu taki sauraron rokon da Patience Jonathan tayi na kar a rufe ma'ajiyanta na $15.591m

- Hukumar EFCC ta nemi kotun da karta fasa rufe ma'ajiyin saboda bincike ya nuna kudaden dake cikin ma'ajiyan sunada maburbuga mara kyau

- Justice Mohammed Idris ya bada umarnin a kara binciken tantance masu kudaden dake cikin ma'ajiyan nata, kuma ya nuna korafe-korafen ta na kare kai bazai kaita ga gaci ba ba tareda dalili ba

Kotun koli ta tarayya a Ikoyi Legas ta ki bada sauraro wa korafin Mrs. Patience Jonathan na kar a rufe ma'ajiyan nata dake dauke da kudade kimanin dalar Amurka $15.591 milyan.

Mai shari'a Justice Mohammed Idris ya bada umarnin kara binciken tantance masu kudaden dake cikin ma'ajiyan nata, kuma ya nuna korafe-korafen ta na kare kai bazai kaita ga gaci ba ba tareda dalili ba. A jawabinsa, “dukkanin zantukar mai kare kanta din basu da dalili karbabbe, kuma babu yanda za'ayi a yarda da hakan a kotun shari'a ."

Mai Shari'an yace ya ganin kotun nan batada yanda zatayi gurin amfani da zanturtukan mai zance a kokarin kare kanta don kuwa zanturtukane da aka ginasu akan rashin ingartaccen dalili karbabbe.

KU KARANTA: Naira ta yi kasa a kasuwar canji

Yace:

“Abin tausayi yanda abu zai kasance sabanin tunanin masu kokarin kare wacca suke karewa, sanin mu ne cewa ita doka bata da kula ko karkata daga wanda baya kan gaskiya a kotun shari'a.”

Justice Idris yace a fadar NAIJ.com a duk sanda ba'ayi shirin tukarar abu da kyau ba to hukuncin dake hawa kan abu baya yin kyau.

Dukkanin kokarin tunkude laifin da akeyi ya kunshi dalilai ne marasa tabbas, a mahangata lafuzzan baki kadai basu wadatuwa batareda takardu na hakika ba dake dauke da bayanai ingantartu ba.

A sakamakon haka kotu ta bada umarni karkashin doka ta 2009 cewa dalilai sun nuna Mrs. Jonathan itace mai ma'ajiyan kuma basu da alaka da ma'ajiyan da ake alakantasu wa kamfanonin.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel