Burin mu muyi fito-na-fito da Buhari a zaben 2019 — Inji PDP

Burin mu muyi fito-na-fito da Buhari a zaben 2019 — Inji PDP

- Jam'iyyar PDP ta ce daram take ta kara da shugaba Buhari a zaben shugaban kasa na 2019

- Makarfi ya ce Jam'iyyar ta shawarci shugaba Buhari da ya sake koma wa Ingila domin duba lafiyarsa

- Makarfi ya zargi gwamnatin APC da boye gaskiyar halin rashin lafiyar shugaban kasar

Jam'iyyar PDP mai adawa ta ce babban burin ta shi ne ta sake fafata wa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.

Jam'iyyar ta PDP bangaren sanata Ahmed Makarfi, ta ce bata goyon bayan kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar ke yi na neman shugaban ya yi murabus domin ya fuskanci jiyyar rashin lafiyarsa.

Sanata Ahmed Makarfi, ya ce PDP ba ta maraba da yin murabus din shugaba Buhari domin ta fi son idan lokacin zaben 2019 ya zo a nuna 'yar kashi.

Burin mu muyi fito-na-fito da Buhari a zaben 2019 — Inji PDP

Shugaba Buhari a lokacin yakin neman zabe

A cewar sa, jam'iyyar PDP na sahun gaba wajen ba wa shugaba Muhammadu Buhari shawarar ya sake koma wa Ingila domin duba lafiyarsa, kuma matakin daya dauka yanzu ya nuna cewa shugaban ya yi amfani da wannan shawara.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun yi raddi ga addu’ar Fani Kayode ga Buhari

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, shugaban jam'iyyar ya kuma ce suna yi wa shugaba Buhari fatan samun lafiya, inda ya zargi gwamnatin APC mai mulki da boye gaskiyar halin rashin lafiyar shugaban kasar tun da farko.

Sanata Ahmed Makarfi, ya ce jinkirin da aka rika yi na komawar shugaba Buhari asibiti ka iya janyo tabarbarewar rashin lafiyar shugaban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel